Home / News / Hakika Aljanu Na Iya Tunzura Mace Ta Aikata Barna – Umar H Kwanar Mai Shayi

Hakika Aljanu Na Iya Tunzura Mace Ta Aikata Barna – Umar H Kwanar Mai Shayi

MALAM Umar Hashim Kwanar Mai Shayi Unguwar Sanusi, cikin garin Kaduna masani a game da al’amuran bincike a kan Magunguna da Tarihin magabata kuma Malamin addinin Islama sannan mai kishin ganin an samu ingantacciyar al’umma da ke da makarantar Koyar da matasa ilimi, ya bayani kan irin lamarin matar da ake ganin ita ta kashe yayanta guda biyu Namiji da mace yan shekaru biyar dakunan mace mai shekaru uku ya kuma yi bayani kan yadda tarbiyya take da kuma karin aure ga duk Namiji a tattaunawarsu da wakilinmu Mustapha Imrana Abdullahi, ayi karatu lafiya.
Garkuwa : Game da matar da ake ta yayatawa cewa ta kashe yayanta ta hanyar yanyankasu da wuka a Kano shin a bisa Mahangar ilimi shin yaya abin yake.
Umar Hashim : Da farko dai zamu ce Innalillahi wa’inna alaihi raji’un, hakika ita wannan baiwar Allah abune da yakamata a tausaya mata a kuma jajanta mata domin ita ce wadda ta yi makudar wadannan yaran kuma ita ce ta dauki dawainiyarsu har suka kai wannan shekaru, amma a karshe wadansu abubuwa suka taso to, bisa hakan a kan samu hanya ta sihiri a Juyar da kwakwalwa.
Domin Allah ta’ala ya fada idan shedan ya ribaceka to ka nemi tsari ga Allah domin lokacin da shedan ya tisgeka zaka iya aikata abubuwa da yawa, kuma idan ka fusata sai ka samu ruwa ka yi alwalla saboda fushi ya kan tashi ne daga garwashin wuta kuma shedan ya kan ingiza mutum ya shiga cikin tashin hankali da turka turka.
Ina tabbata maka duk dadin da Annabi Adamu ya zauna a cikin aljannah ya fita ya bar wannan Ni’ima ta dalilin Shedan amma daga karshe Allah ya karbi tubansa.
sannan maganar Juyewar kwakwalwa mutum ya rasa halin da yake har ya aiwatar da wani abu da za a ce son me ya yi wannan abu ne ba boyayye ba domin Allah ya fadi cewa akwai ranar da Mace za ta manta da abin da ke cikin cikinta sannan kuma mai ciki ta haifar da abin da ke cikin cikinta zaka ga mutane suna maye amma ba su sha Giya ba.
A zamanin akubar Allah ce ita ce ta tsananta saboda haka wannan zai tabbatar maka wannan zai iya faruwa, idan har ya tabbata Jinnu ne hakan zai iya faruwa a firgita mutum tunaninsa ya zamo ya dauke wannan kuma ba karya ba ne domin kur’ani ya tabbatar da hakan sannan idan har aka ce sihiri shima ba karya ba ne domin ya faru ga Manzon Allah wanda ya debi tsawon kwanaki ya kan tambayi inda zai kwana daga cikin iyalansa don haka wannan zai tabbatar maka a kan iya yi wa mutum wani abu da kwakwalwarsa za ta iya daukewa a kuma yi amfani da tunaninsa ya aikatar da abin da zai yi Dana Sani.
Daga cikin tarihi zai yi wahala ko a cikin tarihin magabata ka  ji an ce ga inda Mace ta kashe Danta sai dai abin da yagabata na tarihin magabata shi ne Larabawa idan aka yi masu haihuwa na yaya mata  sukan dauke su suje su haka Rami su rufe su amma Mazan ne ba Mata ba domin mata ba su yarda a dauki yayansu, wannan ya taba faruwa a lokacin bani Isra’ila lokacin daya daga cikin Annabawa wala Allah ko dai lokacin Annabi Musa ko lokacin Suleiman wasu Yan Mata sun ta fi za su yi wanka sun ajiye yayansu guda biyu a lokacin da suka ajiye yayan biyu Zaki ya zo ya dauke na ita wadanda suke wanka to, ashe ya dauki na babbar ne amma da aka fito daga wurin wanka ita babbar sai ta rike Yaron jinjiri ta ce na ta ne ita kuma karamar ta ce ba ta yarda ba ita ma na ta ne suka yi ja – in ja sai gaban Annabi Suleiman, a lokacin da suka je gaban Annabi Suleiman, Alaihissatu wassalam ya tambayesu kowace ta ce da nata ne Annabi Suleiman ya ce sai dai a dauko Wuka domin ayi hukunci lokacin da aka dauko Wukar sai ya ce to za a raba dan nan gida biyu ke ki dauki rabi ita ta dauki rabi nan take karamar ta ce in haka ne ta yafe.
Ba zai faru ba daman a yanka amma hukima irin ta Annabi Suleiman ya yi masu haka sai karamar ta ce ta yafe daga nan sai Annabi Suleiman, ya gane cewa dan ba na babbar ba ne na diyar ne don haka idan ka duba a lokacin da aka haifi Annabi Musa Alaihissalatu wassalam uwarsa da ake kokarin a kashe yaya jira jirai ita Allah ya taimake ta da daukar dan ta Jefa a cikin Teku domin alkawalin Ubangiji ya yi alkawalin zai dawo mata da shi idan.
mun duba duk yadda ake tunani cewa ita wannan mata za ta iya kashe Danta zai yi wahala bosa kamar yadda nagaya maka.
Bari ma in dauko maka kassar wata Jemagiya da abin ya faru a gaba na lokacin da ta debo yayanta tana makale da su a fukafuki a lokacin akwai wani Rami tana son ta shiga amma Ramin sai yaki yuwuwa ta shiga da yayan karshe sai ta zube yayan sai ta shiga cikin Ramin bayan da ta shiga cikin Ramin sai ta sake fitowa da niyyar ta debi yayan.
Amma yawan yayan ta kasa ta shiga karshe dai wannan Jemagiya da yake lokacin Ruwa ne da daddare da sassafe koda aka zo ta Mutu amma ga yayan suna makale a Fukafukinta, Dabba idan ta haifi yaya ta kan yi kokari ta fitar da su amma da wahala ta koma baya domin zoron kar ta taka su juyawa take yi domin ta lashe masu wannan jinin haihuwar don haka wannan baiwar Allah dole ne a tsaya a lura bisa abubuwan da na lissafa maka akwai sihiri na Ture akwai kuma sihiri wanda ake iya hada shi da aljani ya canza mata siffar yaya, dukiya ya kan faru ya fada ga yaya ko mutunci da yaya, saboda haka maganar sihiri abu ne mai sauki wanda dan Adam kan iya shiryawa domin ya cutar da wani, maganar wannan baiwar Allah ta yanka yayanta ko maganar kishi wannan Alal hakika mu da muke gudanar da bincike bisa ga halaye na dan Adam da kuma bincike a kan tarihin magabata bamu ga haka ba don haka ba tunanin wannan mata ta yanka yayanta a tunanin cewa yayanta ne ta yanka wannan hakika akwai abin bincike saboda haka Allah ne kadai zai iya fitar da wannan baiwar Allah ga halin da take ciki saboda duk wanda yake son Da bai kai Uwa ba shi yasa da yawa Uba ya kan Kori dansa amma uwa zai yi wahala ta Kori Danta domin ita kadai ta san wahalar da ta sha, shi yasa aka ce nakuda daya tana matsayin shahada ga duk matar da ta yi nakuda don haka zai yi wahala ace uwa ta kashe yayanta.
Garkuwa : Shin Malam a cikin ayyuka irin na ku na bayar da magani yana hadawa da mata shin kun taba samun wani batu mai kamar haka na tsananin kishi kamar yadda ake ta yadawa domin wasu na cewa don an yi mata kishiya ne ta dauki mataki irin wannan?
Umar Hashim : Hakika, Mata sukan iya yin wani abu da ya shafi kishi sukan yi kokari suga bayan ita kishiyar ko su Jefa mata wata Larura kuma Matan iya yin wani abu da ya shafi hushi kamar yadda na fada. Shiko shedan a lokacin Fushi yake samun dama kamar yadda na gaya maka akwai fushi ba kuma ni ne na fadi ba Kur’ani ne ya fada cewa daga lokacin da ka samu tusguwa irin ta Shedan ka nemi tsari shi kuma Manzon Allah ya ce ka nemi Ruwa ka sanyaya domin fushi ya kan huru ne kamar Garwashi kuma in ya faru babu abin da ba zai iya faruwa ba akwai Kunci shi ne ake cewa Tawatturi akwai kuma Irhak sannan kuma akwai wanda ake kiransa Kalaku mutum yakan fita daga cikin yanayinsa akwai kuma Huzna, akwai Gammmu akwai Hammu dukkansu na’ine na bakin ciki wanda.
Akwai Hammu da Gammu sune ke iya sanyawa mutum ya yi wani abin da bai ta ba tunani ba sai daga baya ya yi Danasani, amma irin wannan Hammu da Gammu bai kama Ummiyya wato uwa har ta yi wa yayanta akwai wanda za ta yi misali ta dauko abin duka ta buga ba ta yi tsammanin cewa ta aikata ba ta kan dawo ta yi Danasani.
Wannan zai baka mamaki daga daya aka je ga biyu, hakika Mata sukan iya samun kishin da za su Kassara Amarya ko ita Amaryar ta nemi ta Kassara uwargida kuma muna samun hakan amma yakan tsaya ga kishin ne sannan kuma ana samun wanda za a yi wa miji don a Kassara shi duka muna samu ko a zuwa Ruwan Zafi a kona shi ko a zuba Fetur a kunna Wuta ko kuma ayi wani abu da za a sa cikin abinci don a Kassara shi to wannan duk ana samu.
Kaga babu wata fa’ida da ake tunanin wanda don shi aka yi kishi kuma a kashe shi to, me zai bayar da fa’ida ga mutumin da ake kishi don shi kuma an kashe shi? kaga kenan an dai jawo bala’i, akwai abin da za a iya yi amma mafi yawa wanda ke faruwa irin wannan a tarihance ba mu taba ji ba ace Uwa ta kashe yayanta ko matan da ake cewa suna kashe yaya zaka tarar wata ce ta samu ciki wanda ba na aure ba wanda wani lokaci Uwarta ce ma za ta kashe, amma ita da ta Haifa zai yi wahala ta kashe da kanta, akwai matsaloli da dama da zai nuna cewa wannan baiwar Allah a kara bincike tukuna kada mutane su fada cikin Tarkon da ba za su iya fita ba, Allah ka kare mu.
Garkuwa : shin akwai wata fadakarwa daga a yi ga magidanta Maza da Mata domin gujewa samun fadawa cikin wata larura irin wannan?
Umar Hashim : Shi ka’idar aure Adalci aka ce ka yi addinin Islama hakika ya bayyana yadda za a yi zaman aure harma a samu rabuwa Kur’ani cewa ya yi ka zauna da ita da adalci da kyautatawa kuma ka sake ta kana mai kyautata mata ba tare da ka musguna mata ba da yawa akwai matan da suke yin aure ma ba su Isa su yi auren mata biyu ba suna da abincin da za su ciyar da Matan amma ba su da tarbiyya da kuma hikima na su zauna da matan guda biyu saboda haka ire iren irin wadannan su kan rusa tarbiyya kuma su rusa zaman gidansu.
Sannan da yawa akwai Namijin da ya kan yi aure ne domin kawai ace yana da mata guda biyu har ma gasa ake yi a filin tattaunawa wannan ya ce kai a zamanka mai Mata daya ka kasa kara Mata wanda kuma ba haka abin yake ba Kur’ani shi ya rigaya ya bada zabi ko biyu ko Uku ko guda hudu idan kana jin tsoron ba zaka iya yin adalci ba domin adalci shi ne jagoranci duk al’ummar da babu adalci a ciki ba za ta iya bayar da abin da ake bukata ba duk Namijin da bai da adalci to gidansa ba zai tashi da kyau ba, ba zai iya tarbiyyar gidan ba domin idan aka haihu hakika zai hada yayansu su zama masu Gaba domin duk abin da kake gani a cikin gida na tabarbarewar tarbiyya da rashin tarbiyya ya tattaru ne a kan Mazaje, karin auren da ake yi idan mutum zai yi adalci gidansa zai zauna ba tare da matsala ba amma daga ranar da ya Sanya rashin adalci ya dauki sirrin wannan ya kai wa waccan duk abin da suka yi da wancan Dakin ya zo ya gaya wa wannan to hakika akwai matsala kuma masu irin wannan bai kamata su hada mata biyu ba domin sune ke Sanya matansu su tsallake kuma suna shiga ta hanyar yi masu bokanci wanda daga nan ne ake samun matsaloli da dama domin ta nan ne ake shirya masu yadda za su cutar da abokanan zamansu yadda ake shirya masu yadda za su cutar da hatta da mijin.
A karshe dai abin da nake fada shi ne abin da Allah ya fadi a cikin littafinsa in kuna tsoron ba zaku yi adalci ba ku zauna da mace guda wannan shi ne hakikanin maganar da ta zo daga sararain Sama daga kuma bakin Allah madaukakin Sarki Adalci shi ne jagorancin gida adalci shi ne jagorancin kamfani adalci shi ne jagorancin Sana’a adalci shi ne jagorancin wadanda ke karkashinka kuma adalci shi ne jagorancin al’umma daga sama har kasa idan babu adalci kamar yadda Allah ya dai daita sama da kasa idan ba domin adalci ba da sai an samu tusgiro a cikin sama da kasa Allah sai da ya dai daita su domin adalci.

About andiya

Check Also

Group Decries Escalation Of  Insecurity In Birnin Gwari

      By; Our Reporter in Kaduna   The Birnin Gwari Progressive Union(BEPU) has …

Leave a Reply

Your email address will not be published.