Home / Ilimi / Kungiyar Kwadago Ta Bukaci A Biya Ma’aikata Hakkinsu

Kungiyar Kwadago Ta Bukaci A Biya Ma’aikata Hakkinsu

Shugaban Kungiyar kwadago ta kasa reshen Jihar Kaduna Kwamared Ayuba Magaji Suleiman, ya yi kira ga Gwamnatin Jihar Kaduna karkashin jagorancin Malam Nasiru Ahmad El – Rufa’i, da ta biya ma’aikatan kananan hukumomi dubu 21 da Malaman makaranta da aka sallama daga aiki harkokinsu.
Kwamared Ayuba Suleiman, ya yi wannan kiran ne a wajen bikin ranar ma’aikata na shekarar 2020, da aka yi a kaduna.
Kwamared Ayuba ya ci gaba da cewa sakamakon irin yadda duniya take ciki na matsalar cutar Korona bairus yasa suka takaita taron ranar ma’aikatan ya zama an gayyaci wadansu shugabannin reshe reshe na yayan kungiyar kwadago domin ayi taron manema labarai a game da ranar.
Don haka muke tunawa Gwamnatin Jihar Kaduna cewa akwai dimbin ma’aikatan da suke neman hakkinsu bayan an sallame su aiki amma har yanzu shuru.
An dai yi taron manema Labaran ne a harabar ofishin kungiyar ma aikatan lafiya da ke kaduna, inda aka fadakar da jama’a cewa bikin ranar ma’aikatan ya samo asali ne daga shekarar 1980 lokacin mulkin Muhammadu Abubakar Rimi lokacin yana Gwamnan tsohuwar Jihar Kano.
Sai Gwamnatin tarayya ta mayar da ranar ta zama ranar hutu a kasa baki daya a shekarar 1981, kuma ranar ma’aikatan ana gudanar da bikin me a kasashe a kalla guda 80 a cikin fadin duniya.
A saboda haka muke kiran Gwamantin Jihar kaduna da ta tabbatar da cika kudirin gwamnati na kiyaye mutunci tare da jin dadin ma’aikata, kamar yadda yake a tsarin kowace gwamnati a duniya.
“Ina son yin amfani da wannan dama in mika cikakkiyar godiya ga Allah Subhanahu wata’ala da ya warkar da Gwamna Malam Nasiru Ahmad El- Rufa’I, kuma ina mika wannan godiya ne a madadin yayan kungiyar Kwadago baki daya”. Inji Ayuba Suleiman.
Ya ci gaba da mika godiya tare da Jinjina ga Gwamnan Kaduna kasancewarsa mutum na farko da ya biya kudin karin albashi na naira dubu 30, sai dai shugaban kungiyar kwadagon ya fadakar da Gwamnati game da bukatar da ke akwai na a rika tafiya tare da kungiyar kwadago a dukkan abin da Gwamnati za ta yi a kan sauran batutuwan da za a yi nan gaba da ya shafi ma’aikata.
“Hakika muna jinjinawa Gwamnati game da irin ayyukan raya kasa da take a cikin garin kaduna na samar da tituna, muna kuma yin kiran da a fadada wannan aiki zuwa yankunan karkara domin a saukakawa jama’a halin da suke ciki, musamman a samar da ingantattun tituna da idan an samu wata matsala da gaggawa irin samun mata masu ciki da sauran matsalolin rashin lafiya a yankunan karkara a samu magance su a cikin sauki”.

About andiya

Check Also

APC RELOCATES TO NEW STATE HEADQUARTERS IN GUSAU, ZAMFARA

The Zamfara State chapter of the All Progressives Congress APC has today relocated to its …

Leave a Reply

Your email address will not be published.