Home / Kasuwanci / Yan Kasuwa A Kaduna Suna Kwashe Kayansu

Yan Kasuwa A Kaduna Suna Kwashe Kayansu

Sakamakon irin yadda duniya ke fama da batun Covid -19 da ake kira da Korona, lamarin da yasa Gwamnatin Jihar Kaduna ta kulle kasuwanni da suka hada da babbar kasuwar kaduna wato Kasuwar Shaikh Abubakar Gumi da ke cikin garin kaduna.
Kamar yadda wakilinmu ya zagaya cikin garin kaduna ya tarar dimbin yan kasuwar da suka hada da maza da mata suna ta kokarin kwashe kayansu daga kasuwar, kasancewar sun shafe kwanaki sama da Talatin kasuwar na rufe.
Kamar yadda wakilinmu ya ji ta bakin wani dan kabilar Igbo da ke da rumfar sayar da Takalmi a cikin kasuwar dan kasuwar ya koka da cewa su har yanzu ba su san inda za su koma ba domin gudanar da kasuwancinsu ta yadda za su samu abin sakawa cikin bakinsa.
Wakilin namu ya kuma ji ta bakin wasu yan kasuwar inda suka shaida masa cewa gara su kwashe kayansu domin barinsu a cikin kasuwar ba zai kara masu komai ba.
Sai kuma wadansu da ke da Tunanin su rika zuwa Makarantun Firamaren da Gwamnatin Jihar Kaduna ta bayyana cewa a rika kai kayan abinci da Magunguna ana Sayarwa wato Kasuwannin Unguwanni.
Wakilinmu yaga irin yadda wasu daga cikin yan kasuwar ke zuba kayansu a cikin motocinsu suna wucewa zuwa gidajensu domin samun mafita daga baya.

About andiya

Check Also

Dangote crashes Diesel price to N1,000 per litre

In an unprecedented move, Dangote Petroleum Refinery has announced a further reduction of the price of diesel from …

Leave a Reply

Your email address will not be published.