Home / News / Matasa Na Da Muhimmanci Wajen Ci Gaban Al’umma

Matasa Na Da Muhimmanci Wajen Ci Gaban Al’umma

Muna Kokarin Jawo Matasa Ne A Ta Fi Tare Da Su – Auwal D Kaya
Imrana Abdullahi
Alhaji Auwal Dahiru Kaya, mai neman takarar shugabancin karamar hukumar Giwa cikin Jihar Kaduna ya bayyana cewa ya shigo Gwagwarmayar siyasa ne domin tafiya tare da matasa a tabbatar masu da irin muhimmancin da suke da shi wajen gina kasa da al’ummarta baki daya.
Auwal Dahiru Kaya ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai a Kaduna.
Auwal Kaya ya ci gaba da cewa nema wajibi ne, amma kuma samu na Allah ne bisa wannan imanin ya fito neman takarar shugabancin karamar hukumar Giwa a karkashin jam’iyyar PDP domin taimakawa daukacin al’ummar karamar hukumar Giwa, Jihar kaduna da Nijeriya baki daya.
Ya kuma bayar da tabbacin cewa ya na da kyakkyawan ingantaccen tsarin samar da ci gaban kowane mutum a fadin karamar hukumar Giwa  don haka yake tabbatarwa da jama’a cewa idan sun bashi kuri’a ya zama shugaban karamar hukuma ba za su yi da na Sani ba ko kadan.
“Za mu yi Gwamnati ta jama’a domin jama’a da za ta ciyar da dukkan al’umma baki daya gaba, wannan ya sa muke da tsare tsare da kyawawan shirye shirye ga bangarorin Noma, tsaro da fannin kiwon lafiyar jama’a da kuma sauran fannoni baki daya, saboda haka muke kira  ga jama’ar karamar hukumar Giwa su ba mu cikakken hadin kai da goyon baya su samu biyan bukata.

About andiya

Check Also

Group Decries Escalation Of  Insecurity In Birnin Gwari

      By; Our Reporter in Kaduna   The Birnin Gwari Progressive Union(BEPU) has …

Leave a Reply

Your email address will not be published.