Home / News / Zan Samar Da Hanyoyin Ci gaba A Karamar Hukumar Kaduna Ta Arewa – Amoke

Zan Samar Da Hanyoyin Ci gaba A Karamar Hukumar Kaduna Ta Arewa – Amoke

Zan Samar Da Hanyoyin Ci gaba A Karamar Hukumar Kaduna Ta Arewa – Amoke
Mustapha Imrana Abdullahi
A kokarin da yake yi na ganin an samar da ingantaccen tsarin gudanar da kananan hukumomi a Jihar Kaduna da Nijeriya baki daya mai Gwagwarmaya domin fadakarwa da kwato yancin jama’a Malam Yusuf Idris Amoke, da ya shiga cikin harkokin siyasa kuma a halin yanzu yake takarar neman kujerar shugaban karamar hukuma Kaduna ta Arewa a Jihar Kaduna ya tabbatar da cewa  karamar hukumar Kaduna ta Arewa na da hanyoyin samun Kudin shiga da in aka yi anfani hanyoyin  zai hana karamar hukumar dogara da Kudin shigar da ake samu daga Gwamnatin tarayya a kowani wata.
“Za mu iya yin amfani da wadannan hanyoyin domin yin koyi da irin yadda Gwamnatin Jihar Legas da Jihar Kebbi suka a wajen Noman Shinkafa inda aka samu biyan bukata, to, a karamar hukumar Kaduna ta Arewa ba mu da filin Noma a wadace amma muna da yawan jama’a don haka za mu yi amfani da hakan domin bunkasa karamar hukumar da ta kasance cibiyar Jiha”.
Honarabul Yusuf Idris Amoke, da ake yi wa taken Gobe Ta Allah Ce, ya bayyana haka ne lokacin shan ruwa bude baki ,da ‘yan Jaridu a Kaduna ya ce ya na da tsari da zai bullo dashi ta hanyar amfani da hanyoyin da suka hada da amfani da Kungiyoyi don karban haraji a saukake ba tare da tsare Mutane da cin zarafinsu don karban Haraji ba,hakan zai rage sulalewar harajin kamar yarda ake gani a baya.
Bugu da Kari, a matsayina na masanin muhalli zan yi amfani da matasa ta hanyar sarrafa Shara don Alkinta tattalin arzikin kasa  zuwa abu mai amfani da zai samar wa da karamar hukumar kudin shiga,kaga kenan zaka ga mata da matasa sun samu abin yi kenan zai zama duk wani Robobi ko ledoji an nema anrasa saboda an an sarrafa  su sun zama kudi.
Daga karshe ya yi kira da ‘yan Jaridu a kan Jaddada Muhimmancin zaman lafiya tare kuma da tunasantar da Shugabanni don samar da kyakkyawan shugabanci da zai magance matsalar tsaro da ke fuskantar sassa dabam- dabam na kasar tarayyar Nijeriya.
Shi kuwa da yake nashi Jawabin Mataimakin shugaban yan Jarida na kasa Shiyar Arewa maso Yamma NUJ Zone A, wanda ya yi magana a madadin yan Jaridun da suka samu halartar taron Kwamarad Yusuf Idris, cewa  yan Jarida a shirye suke na ganin sun goyi bayan ci gaba da mahukunta ke samarwa ga al’ummarsu.
Idris ya kuma yi  kira da cewa kofar yan Jaridu a bude take na yayata abubuwan ci gaba da Shugabanni ke samarwa al’umominsu kasacewar yan jarida masu Sanya idanu domin ganin matakan Hwamnati uku sun aiwatar da aikin da ya dace ta yadda al’umma za su samu biyan bukata.

About andiya

Check Also

Majalisa Ce Ta Bambanta Dimokuradiyya Da Mulkin Karfa Karfa – Ado Doguwa

  …Sai An Ba Kananan hukumomi Yancinsu   Bashir Bello majalisar Abuja Honarabul Alhassan Ado …

Leave a Reply

Your email address will not be published.