Home / Ilimi / AN SAKI RAGOWAR YAN MATAN MAKARANTAR  YAWURI

AN SAKI RAGOWAR YAN MATAN MAKARANTAR  YAWURI

DAGA IMRANA ABDULLAHI
Bayanan da muke samu na cewa yan Ta’adda sun saki sauran ragowar yan matan makarantar kwalejin Gwamnatin tarayya ta yan mata da ke garin Yawuri kashi na  biyu da suka rage a hannun yan Ta’adda.
Yan ta’addan da suka sake yan matan kwalejin Gwamnatin tarayya da ke garin Yawuri a Jihar Kebbi sun sako sauran yan matan da suke tsare da su, kamar yadda jaridar yanar Gozo ta PRNigeria ta wallafa.
Da safiyar ranar Alhamis ne aka saki yan matan.
Kamar yadda rahotanni suka bayyana, Fa’ida Sani Kaoje da Safiya Idris, bayan an yi tsananin tattaunawa an tattare wuri domin sakinsu an yi hakan ne ta hanyar wani kwamitin da aka kafa daga iyalin da kuma masu yi masu fatan alkairi domin sakin nasu, an kuma samu tattaunawa ne da shugaban yan ta’addan.
Shahararren dan ta’addan da ke yi wa sauran jagoranci, Dogo Gide, ya maka kaimin cewa dole ne sai an cika wasu matakan ka’idoji kafin a sake su kuma sharuddan na su Gwamnatin Jihar Kebbi ce za ta cika su kafin a saki sauran wadanda suka rage a sake su.
In dai zaku iya tunawa a ranar 22 ga watan Afrilu ne 2023, jaridar PRNigeria da ake wallafawa a yanar Gizo, ta bayar da rahoton sakin yan matan na makarantar yan mata ta Yawuri guda hudu da jariransu, bayan an biya makudan kudi a matsayin kudin fansa ga Dogo Gide a matsayin shugaban yan Ta’addan da suka kama yan matan.
Wadansu yan satuttuka kuma, a ranar 7 ga watan Mayu sai aka sake sakin wadansu yan matan huda uku kuma da suka hada da Elizabeth Ogechi Nwafor, Esther Sunda da Aliya Abubakar duk yan ta’addan suka sake su.
Nan ma an sake su ne bayan an bayar da makudan kudin fansa kudin kuma an tattara su ne daga yan uwa da abokai tare da uyayen daliban tun bayan da Gwannatin Jihar Kebbi ta yi kunnen uwar Shegu da batun biyan bukatun yan ta’addan da suka sace daliban yan mata.
Iyayen yaran sai da suka yi roko ga yan Najeriya da su kawo masu daukin tallafin kudi domin a saki yayansu daga hannun wadanda suka sace su.
A cikin wata takardar da aka aikewa dukkan yan NajeriY a watan Janairu, 2023, takardar da jaridar PRNigeria ta samu a lokacin, wadda wani kwamitin iyaye na yan makarantar Yawuri 11 da aka sacewa yara” suka rubuta, suna neman taimakon kudi domin tara naira miliyan 100 da za a biya kudin fansa da su ga yan Ta’adda, matsayin kudin fansa, domin a saki yayan nasu.
Shugaba da sakataren kwamitin na iyayen yara, Salim Kaoje da Mista Daniel Alkali, baki daya sun ce yayansu yan mata masu shekaru tsakanin 12 zuwa 16 suna hannun yan Ta’adda na tsawon watanni 20  tun a lokacin da suka fadi maganar.
“Wadanda suka sace yaran na bukatar kudi naira miliyan 100 kafin su saki yaran yan makarantar farin Yawuri”.
In dai za a iya tunawa yara dalibai guda 11 ne aka kama aka kuma yi Garkuwa da su lokacin da yan ta’addan suka kutsa kai zuwa makarantar a ranar 17 ga watan Yuni, 2021.
A watan Nuwamba na shekarar da ta gabata jaridar PRNigeria, ta bayar da rahoton cewa wasu daga cikin yan matan sun zamo iyaye yara, saboda akwai wadansu guda hudu duk sun dauki ciki.
Sai dai kuma jaridar PRNigeria ba za ta iya tabbatarwa da jama’a ko an biya kudin fansa daga iyayen yaran da ko kudin ya kai naira miliyan 100 kamar yadda tun farko yan ta’addan suka bukaci iyayen yaran su biya fansa.

About andiya

Check Also

APC RELOCATES TO NEW STATE HEADQUARTERS IN GUSAU, ZAMFARA

The Zamfara State chapter of the All Progressives Congress APC has today relocated to its …

Leave a Reply

Your email address will not be published.