Home / News / YADDA LAMIDI APAP YA SHA DA KYAR A KOTUN ABUJA

YADDA LAMIDI APAP YA SHA DA KYAR A KOTUN ABUJA

Sakamakon irin yadda al’amura suka kasance tun bayan kammala zaben shugaban kasa na shekarar 2023 da ya gabata, jam’iyyar Lebo ta shiga cikin wani hali na tsaka mai wuya Inda aka samu wadansu bangarori biyu masu ikirarin cewa suke da shugabancin jam’iyyar a mataki na kasa.

Kamar dai yadda lamarin ya kasance wani bangaren da ake cewa shi ne tabbataccen halastaccen shugabancin jam’iyyar Lebo na kasa na karkashin Barista Julius Abure sai kuma wani bangaren da ke ikirarin cewa shi ke da shugabanci karkashin Lamidi Apapa wanda ko a jiya Laraba ya sha ihu daga wasu magoya bayan jam’iyyar da suka halarci harabar kotun da ke sauraren karar da aka shigar ta shugaban kasa.

Kamar dai yadda rahotanni suka bayyana cewa A ranar Laraba, 17 ga watan Mayu, 2023, wanda ya bayyana kansa a matsayin shugaban jam’iyyar Labour Party (LP), Lamidi Apapa, ya sha ihu tare da ba’a a harabar kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa da ke Abuja.
An rika yi masa Ihun “Ole, ole”, “barawo, barawo”, “barawo”, “siyar da yancin sa”, “dan bakin ciki”, “munafuki”, wasu kuma na kiransa“ Dan APC”, da sauransu wanda aka yi furta kalaman yayin da Apapa ke kokarin fita daga cikin kotu jim kadan bayan dage zaman.

Apapa dai jim kadan gabanin kotun ta fara zama a kan shari’ar, ya jagoranci wasu mabiyansa yin rigima a kan kujerun da ‘yan jam’iyyar Lebo za su zauna a zaman kotun.

Lamidi Apapa, wanda tun bayan kammala zaben shugaban kasa ya dade yana neman karbar ragamar shugabancin jam’iyyar, da kyar ya tsallake rijiya da baya yayin da jami’an ‘yan sanda suka yi masa garkuwa, aka kai shi inda motarsa ​​take a wajen harabar Kotun.

Lokacin da Apapa ya yi ƙoƙarin yin magana da ‘yan jarida, an ci gaba da yi masa wulakanci da hana shi magana, wanda hakan ya sa duk abin da yake so ya faɗa bai yi  amfani ba a wurin.

About andiya

Check Also

Dangote cement export of clinker, cement increase by 87.2%

  Management of Dangote Cement Plc has revealed that the company dispatched seven ships of …

Leave a Reply

Your email address will not be published.