Home / Labarai / Dakataccen Gwamnan Bankin CBN Na Hannun Mu – DSS

Dakataccen Gwamnan Bankin CBN Na Hannun Mu – DSS

Hukumar tsaron farin kaya ta DSS a tarayyar Najeriya ta ruwaito cewa yanzu haka hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta kama gwamnan babban bankin Najeriya (CBN) da aka dakatar, Godwin Emefiele.

Wannan dandali na yanar gizo ya kara da cewa hukumar a safiyar ranar Asabar, ta karyata rahotannin kafafen yada labarai cewa ta kama Emefiele, nan da nan bayan dakatar da shi.

Sai dai mai magana da yawun hukumar, Dakta Peter Afunanya, a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter a yammacin ranar Asabar, ya bayyana cewa takatacven gwamnan CBN da aka dakatar a yanzu yana hannun ta.

“Hukumar DSS a nan ta tabbatar da cewa Mista Godwin Emefiele, dakataccen gwamnan babban bankin Najeriya (CBN) na hannun ta saboda wasu dalilai na bincike,” kamar yadda aka rubuta a shafin yanar Gizo na  Twitter.

Sai dai ta umurci kafafen yada labarai da su yi taka-tsan-tsan wajen ba da rahotonsu na musamman.

“An umarci jama’a, musamman kafafen yada labarai, da su yi taka-tsan-tsan a cikin rahoton da labarai game da hakan,” kamar yadda shafin na   tweet ya ruwaito.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.