Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana cewa rikicin cikin gida da kuma taƙaddamar shari’a da ke addabar Jam’iyyar PDP su ne manyan dalilan da suka sa ya yanke shawarar sauya sheƙa zuwa Jam’iyyar APC.
Mataimakin Gwamnan Jihar Zamfara, Malam Mani Mummuni, ne ya sanar da sauyin sheƙar a hukumance a ranar Litinin, bayan wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a Gidan Gwamnatin Jihar da ke Gusau.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, an bayyana cewa sauyin daga Jam’iyyar PDP zuwa APC ya zama dole domin kare muradun al’ummar jihar baki ɗaya.
Sanarwar ta jaddada cewa matakin shiga Jam’iyyar APC ya biyo bayan shawarar da manyan masu ruwa da tsaki na siyasa a Jihar Zamfara suka cimma, sakamakon matsalolin shari’a da rikice-rikicen da ke addabar PDP a halin yanzu.
Sanarwar ta ce, “A jiya ne Gwamna Dauda Lawal ya sanar a hukumance cewa ya fice daga Jam’iyyar PDP tare da komawa Jam’iyyar APC, matakin da dukkan masu ruwa da tsaki a Zamfara suka amince da shi bayan tattaunawa mai zurfi.
“Gwamna Lawal ya nuna cikakken jajircewa da biyayya ga Jam’iyyar PDP tun tsawon lokaci, inda ya yi ƙoƙari matuƙa wajen sasanta rikice-rikicen da ke tsakanin bangarorin jam’iyyar domin tabbatar da haɗin kai da kuma damar tsayar da ’yan takara a zabukan da ke tafe.
“Sai dai duk ƙoƙarin da aka yi na samar da zaman lafiya, sulhu da warware matsalolin ba tare da zuwa kotu ba bai yi nasara ba, lamarin da ya haifar da jerin shari’o’i a kotuna, waɗanda ka iya yin tasiri ga shugabannin da za su tsaya takara a zaɓen shekarar 2027.”
Sanarwar ta kuma bayyana cewa Gwamna Lawal shi ne mutum na ƙarshe daga cikin manyan shugabannin PDP da ya tsaya tsayin daka a cikin jam’iyyar har zuwa lokacin da hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara ya fito.
A cewar sanarwar, shi kaɗai ne gwamna mai neman wa’adi na biyu da ya ci gaba da zama a PDP har zuwa ƙarshe, yana fatan shugabannin jam’iyyar za su nuna ƙwarewa da ɗaukar matakan da suka dace domin warware rikicin da ke cikinta.
Sanarwar ta kuma nuna cewa a jerin tarurrukan da aka yi na tsawon makonni, Gwamna Lawal ya shaida wa masu ruwa da tsaki cewa ya fahimci buƙatar da suka gabatar na komawa APC, amma zai yanke hukunci ne bayan fitowar hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Abuja.
Kotun ta yi watsi da ƙarar da Jam’iyyar PDP ta shigar kan hukuncin da Mai Shari’a James Omotosho na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ya yanke a ranar 31 ga Oktoba, wanda ya hana Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) amincewa da sakamakon babban taron jam’iyyar na ƙasa da aka gudanar a Ibadan, Jihar Oyo, tsakanin 15 zuwa 16 ga watan Nuwamba.
Sanarwar ta ce, hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙarar ya kawo ƙarshen zaman Gwamna Lawal a cikin Jam’iyyar PDP, inda ya zaɓi shiga Jam’iyyar APC domin bai wa muradun Jihar Zamfara fifiko, tare da ci gaba da aiwatar da manufofin Zamfara ceto da sake gina jihar.
THESHIELD Garkuwa