Daga Imrana Abdullahi
A kokarin da yake yi na ganin an samar da dawamammen zaman lafiya a tsakanin al’ummar Musulmi da Kirista, fitaccen dan gwagwarmayar kwatar wa jama’a hakkinsu kuma mai neman tsayawa takarar Sanatan Kaduna ta tsakiya a Jihar Kaduna Kwamared Shetima Usman Yerima, ya shirya wa Musulmi da Kirista taron shan ruwa a gidansa da ke Kaduna.
Shetima Usman Yerima ya dai gayyato shugabannin al’umma da dama tare da shugabannin addinin Musulunci da na Kirista inda bayan an sha ruwa Musulmi suka gudanar da Sallar magariba, sannan aka ci gaba da cin abinci da abin sha da aka tanadar wa baki a wannan wurin inda gidan ya cika makil da jama’a har waje.
Da yake gabatar da jawabi a wajen mutumin da ya gayyato daukacin al’ummar Shetima Usman Yerima, ya ce bisa la’akari da cewa lokacin yin Azumin watan Ramadan na Musulmi da kuma azumin Kiristoci yazo dai dai lokacin guda sai ya ga dacewar lallai a wannan shekarar ya gayyaci shugabannin addinin Musulunci da na Kirista domin a hadu tare don jaddada zaman lafiya da kwanciyar hankali a tsakanin al’umma.
“Na samu tsawon shekaru Goma sha Uku ina yin wannan taron shan ruwa na jama’a don haka wannan mun dai dan yi wannan gayyatar ne na shugabannin addini domin kara jaddada hadin kai a tsakanin al’umma baki daya”.
Shetima ya kara da cewa hakan yasa muka gayyaci Malam Shaikh Dokta Ahmad Abubakar Gumi da kuma Rabaran John Joseph Hayaf daga kungiyar kiristocin Najeriya shiryar arewa domin su zo su yi wa jama’ar da suka taru jawabi a game da muhimmancin zaman tare da samun hadin kan Musulmi da Kirista a Najeriya baki daya.
Da yake tofa albarkacin bakinsa Sheikh Dokta Ahmad Abubakar Gumi cewa ya yi yana kara fadakar da al’umma muhimmancin samun zaman lafiya tsakanin dukkan al’umma baki daya.
“Ina kuma kara fadakar da Musulmi masu yin azumin watan Ramadana da cewa su sani da an zo lokacin da za a kara kaifin yin ibada domin neman dacewa da Daren Lailatulkadari mai albarka don haka jama’a lallai kowa ya dage don neman dacewa.
A nasa jawabin Rabaran John Joseph Hayaf, fadakarwa ya yi ga masu yin wani tunani game da hadin kan al’ummar Musulmi da Kirista da cewa su canza tunani domin lokacin da kowa ya gane ake hada kai lallai ya yi.
“Ku duba fa a da can sai a rika cewa ta yaya Kirista zai je gidan Musulmi har ya ci abincinsa amma duk kunga wannan ba haka ba ne ga mu a nan cikin gidan Musulmi mun kuma yi bude baki tare wannan duk alamar hadin kai ne a tsakanin juna don haka kowa ya gane inda aka dosa”.
Jama’a da dama dai sun tofa albarkacin bakinsu a wurin taron da shuka hada da Dokta Abdullahi na kungiyar fafutukar fadakarwa da inganta rayuwar jama’a da dai sauran wadansu manyan bakin da suka hada da shugaban jam’iyyar Kaduna ta Arewa da suka halarci taron.
THESHIELD Garkuwa