Home / News / 2023: Yan Kishin Kaduna Ta Tsakiya Sun Goyi Bayan Sardaunan Badarawa Da Zama Sanata Shiyyar

2023: Yan Kishin Kaduna Ta Tsakiya Sun Goyi Bayan Sardaunan Badarawa Da Zama Sanata Shiyyar

Daga Wakilin mu
A YAYIN da babban zabe na shekarar 2023 ke gabatowa, wata kungiya da aka fi sani da Yan Kishin Shiyyar Kaduna Tsakiya ( Kaduna Central Patriots), ta sha alwashin tattara mutane da kayan aiki don tabbatar da tsohon Shugaban rikon kwarya na karamar hukumar Kaduna ta Arewa Honarabul Usman Ibrahim, wanda aka fi sani da Sardaunan Badarawa ya zama zababben Sanatan Kaduna ta shiyya na biyu.
Shugaban kungiyar siyasa wacce galibi ta ke da mutane daga bangarori daban-daban, Ustaz Bala a wata sanarwa ga manema labarai ya ambaci nasarorin da Ibrahim ya samu a matsayinsa na Shugaban Kaduna ta Arewa na rikon kwarya wanda suka hada da sake fasalin Garagin Mando, yin garambawul ga sashen hukumar ilimin cikin gidan yadda ya kamata, bayar da tallafin karatu ga daliban da suka fito daga gidajen marasa karfi, da sauransu.
Ya kara da cewa ayyukan da Sardaunan Badarawa yake yi na bunkasa rayuwar ‘yan adam ta fannin horar da daruruwan matasa kan sana’o’i daban-daban kamar, aikin kafinta, walda, noma, kiwon kaji da kuma dinki wani abu ne muhimmi, kana yana mai bayyana cewa duk wadanda suka ci gajiyar shirin daban-daban an ba su kayan tallafi don ba su damar dogaro da kai sannan da yuwar suna iya ɗaukar ma’aikata a nan gaba.
Bala, ya bayyana zaben da ke tafe a shekarar 2023 a matsayin wani fagen zabe wanda mutane masu kima da kyawawan halaye na aiki ga al’ummomin su ne kawai za su bunkasa, yana mai karawa da cewa zamanin da ‘yan siyasa ke dogaro ga iyayen gida, manyan jam’iyyu da dimbin karfin Kudin su don cin zabe ya wuce.
“Masu neman takara wadanda ke da alhaki a siyasance ba za su sami wata kafa na cin zabe da har za su hau kan duk wata kudirinsu na hawa saman ba saboda masu zaben sun kara wayewa tare da ci gaban dimokiradiyyar Najeriya da karin wayewar kai da sanin ya kamata.”
” A yanzu mutane suna iya gani da kansu da kuma gane masu barkwanci daga ainihi ‘yan siyasan da ke da kishin ci gaban jama’arsu ko ke ingiza su da gina wasu abubuwa masu dorewa wadanda za su iya wuce su idan basu samu damar ba a wannan lokacin.”
“Masu jefa kuri’a sun fahimci cewa ‘yan siyasar da ke jefa kudi don sayen kuri’u su ne mafiya hadari daga cikin mutane wadanda tsarin aikinsu shi ne yin watsi da masu zaben bayan hakarsu ta cimma ruwa har sai zuwa wani lokaci na zabe sannan za su sake lalubarsu.”
“Za a iya tabbatar da shugabanci na gari ta hanyar yin dubi da ayyukan magabata ta hanyar rahotan irin nasarorin da aka samu ko dai a matsayinsu na jami’in gwamnati ko na masu zaman kansu da aka sanya a cikin al’umma.”
“Dole ne in fada muku cewa San-Turakin Hausa wanda muke kira da Sardaunan Badarawa a cikin da’irarmu ya bambanta kansa da sauran mutane wajen bunkasa mutanensa da kuma samar da ababen more rayuwa ta yadda masu cin gajiyar ba su da kyakkyawar hanyar nuna godiya face yin aiki tare don tabbatar da cewa ya samu zababben mukami inda zai samu damar yi wa mutane aiki.”
“Mun kudiri aniyarmu ne a matsayinmu na masu kishin kasa wadanda ke son ci gaban mutanenmu da al’ummarmu a yankin Sanatan Kaduna ta Tsakiya, shi yasa muka yanke shawarar yin aiki da kowa ta hanyar hadin kai don ciyar da arzikin siyasa na Sardaunan Badarawa da kuma tabbatar da cewa shi ne ya zama sanatanmu na gaba a zaben shakara 2023, “in ji Bala.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.