Home / Labarai / Yan Jarida Sun Ziyarci Wurin Da Ake Aik8n Samar Da Manyan Magudanan Ruwa Da Ke Mabera A Sakkwato

Yan Jarida Sun Ziyarci Wurin Da Ake Aik8n Samar Da Manyan Magudanan Ruwa Da Ke Mabera A Sakkwato

Yan Jarida Sun Ziyarci Wurin Da Ake Aik8n Samar Da Manyan Magudanan Ruwa Da Ke Mabera A Sakkwato

 

 

A yarin wanda Injiniya Kabiru Shikkau ya jagoranta domin ganewa idanuwansu yadda aikin samar da Ingantattun magudanun Ruwa ke gudana a Unguwar Mabera ya yi nasarar ziyartar wurare kamar haka, Mabera Kantin-sani, Maber-Iddi, Mabera-Jelani, Tamaje, Nakasarin-Ardo, Nakasarin-Bare-Bare kuma Maberar-Mujayaamong da sauran wasu wuraren.

 

 

A lokacin ziyarar, manema labaran sun samu zantawa da wasu daga cikin mazauna Unguwar ta Mabera, inda a nan ne suka yaba da yadda aikin ke tafiya cikin tsari tare da inganci.

 

 

A lokacin da su ke yabawar, sun jinjinawa Gwamnatin jahar sokoto, karkashin jagorancin Maigirma Gwamnan jaha, Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal, CFR (Matawallen Sokoto) a kan kokarin da gwamnatinsa ta yi na ganin cewa ta kawo karshen matsalolin cushewa da ambaliyar-ruwa da ke addabar wadansu wurare a Unguwanni.

 

 

Mazauna Unguwar ta Mabera, sun kuma jinjinawa Kwamishinan Ma’aikatar Kula da Muhalli na Jaha, Honarabul Sagir Attahiru Bafarawa a kan kokarin da ya ke na ziyartar wuraren da ake gudanar da aikin akai-akai, tare da sauraron korafe-korafen su domin samun nasarar wannan aiki da ake yi a Mabera.

 

 

Cikin wadanda aka yi zagayen tare dasu sun hada da Babban Mataimaki Na Mussaman ga Gwamnan jahar Sokoto, Honarabul Yusuf Dingyadi da jami’in hulda da yan’ jarida na shirin NEWMAP a Jihar Sakkwato, Malam Jamilu Abdullahi, da kuma Jami’in Watsa Labarai na Ma’aikatar Kula da Muhalli na Jaha, Abubakar Abdullahi (Ghani Abdullahi).

 

 

Sai Wakilan kafofin watsa labarai na cikin gida da dama suka halarci zagayen har da na wakilan kafofin yada labarai masu aiko masu labari daga Jihar Sakkwato.

 

 

About andiya

Check Also

Majalisa Ce Ta Bambanta Dimokuradiyya Da Mulkin Karfa Karfa – Ado Doguwa

  …Sai An Ba Kananan hukumomi Yancinsu   Bashir Bello majalisar Abuja Honarabul Alhassan Ado …

Leave a Reply

Your email address will not be published.