Home / Big News / GWAMNAN BAUCHI YA RATTABA HANNU KAN WASU DOKOKI UKU 

GWAMNAN BAUCHI YA RATTABA HANNU KAN WASU DOKOKI UKU 

GWAMNAN BAUCHI YA RATTABA HANNU KAN WASU DOKOKI UKU
Gwamna Bala Muhammad Abdulkadir na jihar Bauchi a ranar Laraba ya rattaba hannu Kan kudiri guda Uku wadda Majalisar Dokoki ta aike  Masa domin  su zama doka
Yan majalisar  sun Kuma bukaci cewa wadannan dokoki  da a aiwatar dasu.
Wannnan Kudirin doka sun hada
da
-Gina Makarantar  Karo ilimi kan al’amuran  man fetur da Iskar Gas { Institute of Oil and Gas Alkaleri}
-Doka Kan dashe-dashen Itatuwa da yaki kwararowar hamada da zaizayar  kasa.
An Kuma hada’ Ma’aikatar kula da zuba jari “Investment Corporation” da Bauchi “Investment Promotion Agency” a guri daya.
Bayan Maigirma Gwamna yarattaba hanu Kan dokokin a dakin taro na Gidan Gwamnati, Gwamna Bala Muhammad yace wadannan kudirori zasu taimaka wajen tsare-tsare ta yadda zai taimaka wajen tafiyar da harkoki.
Makaratan horar da ilimin man fetur da Iskar Gas yace Gwamnatin jiha ta yanke hukunci  da hadin gwiwar Gwamnatin Tarayya da sauran manyan hukumomi na duniya don Samar da aihin ingantaccen Ma’aikata don tabbatar da ansamu albarkatun man fetur da Iskan Gas da ake tonowa.
Yace Gwamnatin jiha zatayi aiki da sauran hukumomi da Ma’aikatan man fetur da iskar Gas na ganin wannann makarantar hararwan zata Samar da aihin nagartattun Ma’aikata dazasu zashiga aikin da akeyi na Samar da wutar lantarki a Mambila.
Gwamnan yakara dacewa wannnan Kudiri da yasa ka hanu akai Kan Muhalli anyi shine don kare al’ummah daga shiga zaixayar kasa da sauran aihin matsaloli dasuka shafi Muhalli da lafiyar su.
Wadannan Kudirori damuka tabbatar dasu a yau bakaramin cigaba bane wa Nigeria da jihar Bauchi, Muna Kara godiya wa membobin Majalisa na aiki tare da Kuma hangen nesa dasuke dashi.
Kakakin Majalisa Muna alfahari dakai, na Zama Shugaban kakakin Majalisa jihohi na Nigeria , Jihar Bauchi zamu baka dukkan goyon baya don kayi Nasara.
Gwamnan yakara tabbatar da kudirin Gwamnatinsa na cigaba da aiki da sauran bangarorin Gwamnati don Basu damar aiwatar da ayyukan Cigaba don al’ummar jiha su anfana.
Kakakin Majalisar jiha, Rt.Honourable Abubakar Y. Sulaiman shi Yajagoranci sauran manyan Shuwagabannin Majalisar zuwa gidan Gwamnati don Mika kudirin yazama doka, yace Majalisa zata cigaba da aiki da bangaren zartarwa matukar zata dunga bijiro da kudirori  wadda zai shafi rayuwar Al’ummar jihar Bauchi Kai tsaye.
Maigirma Gwamna, yau gamu Gareka don mu mika maka kudirori uku don ka rattaba musu hanu su Zama doka wadda duka sunada amfani matuka wajen kawo cigaban jihar.
 Jamilu Barau Daga Bauchi.

About andiya

Check Also

Majalisa Ce Ta Bambanta Dimokuradiyya Da Mulkin Karfa Karfa – Ado Doguwa

  …Sai An Ba Kananan hukumomi Yancinsu   Bashir Bello majalisar Abuja Honarabul Alhassan Ado …

Leave a Reply

Your email address will not be published.