Home / News / AYU YA BUKACI FUSATATTUN YAN JAM’IYAR PDP SU TSAME IYALAN SA DAGA HARKAR SIYASA.

AYU YA BUKACI FUSATATTUN YAN JAM’IYAR PDP SU TSAME IYALAN SA DAGA HARKAR SIYASA.

 

Shugaban jam’iyar PDP na kasa Dr. Iyorchia Ayu ya bukaci wasu yan jam’iyar da suke ganin an bata musu rai su tsame iyalansa daga batun da ya shafi siyasa gameda tirka-tirkar shugabancin sa da suke adawa da shi a jam’iyar.

 

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata takarda mai dauke da sa hannun Simon Imobo-Tswam, Mataimaki na musamman ga shugaban jam’iyar PDP na kasa a fannin yada labarai wadda aka rabawa manema labarai.

 

Ya yi wannan rokon ne a lokacin da yake yiwa manema labarai bayani a karshen taron kwamitin amintattu na musamman da ya gudana a sakatariyar jam’iyar dake Abuja.

Rokon na Ayu na zuwa ne bayan da Gwamna Nyesom Wike ya yi wasu kalamai na cin fuskar sa inda ya shigar batun iyalansa a tirka tirkar da ake.

Wike dai yayi zargin cewa Ayu ya karɓi N100m daga wani gwamna mai ci domin sauya mazaunin cibiyar jam’iyar (Peoples Democratic Institute, PDI), kuma ya sake za gayawa ya karbi irin wannan kudin a wajen jam’iya da sunan yin wannan aiki.

Kuma Wike ya kara da cewa ‘ya’ yansa ma idan suka ji abinda yake aikatawa sai sun barranta kansu da shi. (Ayu).

Amma Ayu yace: “tunda shugaban kwamitin amintattu ya yi magana, bai kamata in ce wani abu ba. Amma kuma tunda wadannan zarge zargen sun wuce gona da iri, ina amfani da wannan dama domin warware zare da abawa.” Gameda da zargin sa na farko kuma, wato na karbar biliyan 1, ba zan ce komai ba, saboda kada a tayar da wani ɓalli a jam’iya. Saidai duk da haka ina son a sani cewa babu inda na amshi biliyan 1 daga hannun wani mutum, da sunan ina shugaban jam’iya.

“Kalaman cin fuska dakuma kokarin tozarta ni tun bayan kammala zaben fidda gwanin da ya gudana a 32 ga watan Mayu, da gangan yake yi su kuma abin mamaki ne. A matsayi na na shugaba a jam’iya, dole in yi abinda zai samar da masalaha. Duk da haka kuma idan abun ya fara taba iyali na da mutunci na har ana kokarin wasa da hankalin ahali na, ya zama wajibi in maida martani.

“A saboda haka, ina kara jaddada cewar babu wanda na amshi biliyan daya a hannun shi. Kuma Naira miliyan 100 da wani gwamna ya bada tallafi an yi amfani da su daidai yadda ya kamata. Kuma nan da yan kwanaki kadan za a zo domin Ƙaddamar da PDI din. A cewarsa

Ayu ya kara da cewa “a lokacin da muka zo akwai karancin kudi a jam’iyar, shine dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyar ya bada shawarar a dauki bashin banki na Naira biliyan daya, kuma mai Bankin daya ne daga cikin yayan jam’iyar PDP, duk da yake yanzu ya bar jam’iyar.

Amma a lokacin da muka tattauna da shi, bamu aminta da shawarar ba. Kuma jam’iya ba ta ci bashi daga banki ko wani mutum ba,. Duk wani kudi da aka samu a jam’iyar an yi bayanin sa dalla dalla ga majalisar zartaswa ta jam’iyar kuma aka mika shi ga magajin jam’iya.

A yayin da yake kara jaddada matsayar shi na yin adalci da daidaito a fannin da ya shafi kudi a jam’iyar, Ayu yace:” asusun jam’iyar a bayyane yake, kuma mun yi alkawarin bayar da bayanan duk kudaden da suka shiga da fita, a karshen shekara.

A zarge zargen da yayi a yau yace —” Naji dadi yace, na yi bayani ga kwamitin cewa wani gwamna ya bada tallafin miliyan dari na gyaran PDI, kuma mun yi bayanin cewa mun yi hayar wani waje a Asokoro, kuma muka gyara shi.

A kwanaki biyu zuwa uku da suka gabata, munje kuma mun duba aikin. Kuma NWC sun yanke shawarar kafin kaddamarwar za mu gayyaci gwamnan da ya bada tallafin ya zo ya duba abinda aka yi da kuɗin. Kuma ina farin cikin sanar da cewa tuni sakataren jam’iyar ya aika masa da wasika.

“A saboda haka, ba gaskiya bane. Babu wani kudi da Ni kokuma NWC suka dauka daga asusun jam’iyar domin yin wannan gyara. A halin yanzu ma bamu ƙarar da wannan Naira miliyan 100 ba da gwamnan ya bayar.” a cewar Ayu.

 

 

 

About andiya

Check Also

Dangote crashes Diesel price to N1,000 per litre

In an unprecedented move, Dangote Petroleum Refinery has announced a further reduction of the price of diesel from …

Leave a Reply

Your email address will not be published.