A tarayyar N8jeriya an samu karin mutane 10 masu dauke da cutar korona, an dai samu karin ne a babban birnin tarayya Abuja, Legas da Jihar Edo.
Samuwar wannan adadi an samu mutane dari 224 kenan masu dauke da wannan cutar a duk fadin kasar baki daya
Hukumar yaki da hana yaduwar cututtuka ta kasar ( NCDC) ce ta bayyana hakan a ranar Lahadi.
Hukumar NCDC ta sanar da hakan ne a shafinta na tuwita #covid19 inda suka bayyana cewa an samu mutane 6 a Legas mutane 2 a Babban birnin tarayya Abuja da kuma mutane 3 a Edo.