Home / Labarai / ABUBUWAN DA TALAKAWAN ZAMFARA KE BUKATA – NAFARU

ABUBUWAN DA TALAKAWAN ZAMFARA KE BUKATA – NAFARU

HONARABUL BASHIR NAFARU, Talatar Mafara da ke cikin Jihar Zamafara ya bayyana irin abubuwan da talakawan Jihar ke bukata wajen sabuwar zababbiyar Gwamnati karkashin jagorancin Gwamna Dokta Dauda Lawal.

Honarabul B Nafaru, ya ce bayan mika cikakkiyar godiya ga Allah madaukakin sarki da ya ba su wannan Gwamnatin, “abu na farko shi ne muna son a samu tabbataccen zaman lafiya da kwanciyar hankali duk da mun san Allah ne ke bayar da zaman lafiya duk da haka muna neman Gwamnati ta kara da na ta ikon a samu cikakken zaman lafiya”.

Sai kuma batun karancin ma’aikata a Jihar Zamfara don haka nan ma muke rokon kasancewar akwai yan Boko da yawa ga kuma yan kasuwa, muna rokon Gwamna Dauda Lawal da ya tabbatar da ciyar da ilimi gaba ya kuma dauki ma’aikata ta yadda za a samu aikin yi a wadace a duk fadin Jihar bakai daya.

Sannan kuma muna kara yin roko a kan a taimakawa Talakawa manoma da Takin zamani kowa ya samu a yi Noma a wadace a Jihar Zamafara.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.