Home / KUNGIYOYI / MUNA KIRA GA JAMA’A SU ZAUNA LAFIYA 

MUNA KIRA GA JAMA’A SU ZAUNA LAFIYA 

Daga Imrana Abdullahi, Kaduna Arewacin Najeriya

Shugaban kungiyar tuntuba ta arewacin Najeriya (ACF) na Jihar Kaduna Lawal Umar Mayere, ya yi kira ga daukacin al’ummar Jihar Kaduna musulmi da Kirista da su tabbatar da zaman lafiya tsakanin Juna da nufin ci gaban Jihar da kasa baki daya.

Lawal Umar Mayere ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai a gidansa jim kadan bayan kammala Sallar idi a garin Kaduna.

“Babban al’amari dai shi ne tsoron Allah wanda zai kasance a matsayin sahihiyar hanya ce ta ci gaban jama’ar Jihar Kaduna da kasa baki daya”, inji shi.

Shugaban kungiyar tuntuba ta arewacin Najeriya reshen Jihar Kaduna Lawal Umar Mayere, ya kuma fadakar da jama’a su ci gaba da yin kabbarbarin da addinin Islama ya yi horo ayi bayan kammala Sallar babbar Sallah da ake yanka raguna da sauran Dabbobi da musulunci ya amince da ayi”.

Ya kara da cewa kamar yadda ma’anar yankan layya take a tushen ta shi ne sadaukarwa don haka a tabbatar ana sadaukarwa da nufin samun ciyar da kasa gaba.

Ya dace jama’a su rika taimakon Juna, kaunar Juna tare da rungumar juna a koda yaushe.

A kuma rika samun fahimtar Juna domin maganin fitina tsakanin Juna, a kuma rika ba mutane uziri, kuma shugabanni ba tsinuwa da zagi suke bukata ba suna neman addu’a ne a kuma so Juna a fahimci Juna tare da tsoron Allah.

” Allah ya halicce mu kuma ya na Kaunar juna don haka musulmi da wadanda ba musulmi ba duk bayin Allah ne da kowane yare duk tushe daya ne don haka a kyautatawa juna zato tare da kauna bayan fahimtar junan”.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.