Home / KUNGIYOYI / A KARKATA TALLAFIN RAGE RADADIN CIRE TALLAFIN MAI A BANGAREN MAN FETUR – AMINU GORONYO

A KARKATA TALLAFIN RAGE RADADIN CIRE TALLAFIN MAI A BANGAREN MAN FETUR – AMINU GORONYO

Daga Imrana Abdullahi, Kaduna

Aminu Ibrahim shugaban kamfanin A S Goronyo a bangaren Keke – Napep kuma shugaba na yan Keke – Napep a Jihar Kaduna, ya ce a zahirin gaskiya kamar yadda Gwamnati ta ce za ta bayar da tallafi abu ne mai kyau don haka a irin tunani na da mahangata ace Gwamnati za ta ba mutum naira dubu Takwas (8000) a wata ba fa a kullum ba me za ta yi wa mutum?

Aminu Ibrahim ya bayyana hakan ne a lokacin da yake amsa tambaya daga wakilin mu ta manhajar dan dalin Sada zumunta na Whattsapp.

A matsayin mutum na magidanci kai koma ba magidanci ba ma me wannan kudin zai yi wa mutum a wata?

“Ni shawarar da zan bayar kudin da ake ganin za a bayar da a karkata su a bangaren Mai domin idan an samu sauki a bangaren mai hakika ina tunani zai fi bayar da kudin da za a yi”, inji Aminu Ibrahim.

Dafatan Allah ya kawo mana ci gaba a kasa Najeriya arziki ya inganta ya yadu a ko’ina kowa ya samu sa’ida, shugabannin da muka zaba Allah ya iya masu da iyawarsa ya kuma ba su ikon yi wa kowa adalci da alfarmar shugaba Annabi Muhammadu (S AW).

Indai za a iya tuna wa a tarayyar Najeriya Gwamnatin kasar ta cire tallafin man fetur da a can baya take bayarwa domin samawa jama’a saukin harkokin rayuwa, amma tun da aka cire wannan tallafin komai ya zama Alakakai sakamakon samun hauhawar farashin kayan masarufi da sufuri da na al’amuran yau da kullum abin da yasa kowa ke ji a jikinsa.

Hakan yasa Gwannatin kasar ta kafa kwamitin da zai yi aikin bayar da tallafin kudin rage radadin tallafin da shugabannin majalisun kasar biyu suka ce za a bayar da kudi naira dubu Takwas ga wadanda Allah ya ciyar na tsawon watanni shidda daga lokacin da aka fara bayar da tallafin ga mutane musamman marasa karfi a cikin al’umma.

Sai dai jama’a da dama na bayanin cewa ko ta yaya Gwamnatin za ta iya gano mutanen da ya dace a ba tallafin?

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.