Home / Labarai / SAKON TAYA MURNA ZUWA GA SABON SHUGABAN APC NA KASA GANDUJE MURNA

SAKON TAYA MURNA ZUWA GA SABON SHUGABAN APC NA KASA GANDUJE MURNA

DAGA IMRANA ABDULLAHI

Jam’iyyar APC reshen Jihar Zamfara karkashin jagorancin shugabanta Honarabul Tukur Umar Danfulani na taya sabon shugabanmu na kasa Dokta Abdullahi Umar Ganduje murnar zama shugaban jam’iyyarmu mai girma a yayin babban taron jam’iyyar karo na 12 da ya gudanar yau a Abuja.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwar da ke dauke da da hannun Yusuf Idris Gusau Sakataren Yada Labarai na APC a  Jihar Zamfara da aka rabawa manema labarai.

Ko shakka babu kasancewar tsohon  gwamnan jiha ta biyu mafi yawan al’umma a kasar nan shaida ce da ‘yan Najeriya musamman ‘ya’yan jam’iyyar ke da yakinin cewa zai iya tafiyar da al’amuran jam’iyyar don a samar wa da  ribar dimokuradiyya.

Takardar da aka fita ta ce “Imaninmu ne cewa fitowar ku zai inganta dimokuradiyyar jam’iyyar cikin gida da kuma da’a a tsakanin amintattun jam’iyyar a kowane mataki”.

Sanarwar ta kara da bayanin cewa “Jam’iyyar za ta shaidi sauye-sauyen ci gaba wanda zai dauki nauyin komai kamar yadda ya yi a lokacin da yake gwamnan jihar Kano”, inji sanarwar.

Mu daga Jihar Zamfara muna kara jaddada goyon bayanmu ga shugabancin jam’iyyar da kuma jagorancin jagoranmu na kasa kuma shugaban tarayyar Najeriya mai girma Bola Ahmed Tinubu GCFR.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.