Home / News / GANDUJE ZAI SAKE GYARA JAM’IYYAR APC – KAILANI MUHAMMAD

GANDUJE ZAI SAKE GYARA JAM’IYYAR APC – KAILANI MUHAMMAD

Daga Imrana Abdullahi

An bayyana sabon shugaban jam’iyyar APC Dokta Abdullahi Umar Ganduje a matsayin wanda zai jajirce wajen gyaran jam’iyyar APC domin Najeriya ta ci gaba da bunkasa.

Bayanin hakan dai ya fito ne daga bakin shugaban gamayyar kungiyoyin APC da suka yi fafutukar ganin shugaba Bola Tinubu ya samu nasarar lashe zabe a karkashin jam’iyyar APC, Injiniya Dokta Kailani Muhammad.

Injiniya Dokta Kailani Muhammad ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai a Abuja bayan kammala zaben shugaban jam’iyyar.

Dokta Kailani muhammad ya ci gaba da bayanin cewa “sauran wadansu shugabannin APC da suka gabata Allah ya raka taki Gona, amma shi wannan Abdullahi Umar Ganduje mun yi magana da shi kuma ya tabbatar mana da cewa zai shiga gyaran jam’iyyar ne ka’in da na’in babu kama hannun yaro don haka ya dace kawai a bashi cikakken hadin kai da goyon baya domin kwalliya ta biya kudin sabulu”.

Ya ce ” sabin shugaban jam’iyyar Dokta Abdullahi Umar Ganduje zai bi daukacin yayan jam’iyya da sauran jama’a gida gida, Kananan hukumomi da Jihohi domin jawo jama’a da kuma ba su hakuri ga duk wanda yake ganin an bata masa domin a ta fi tare”.

Kailani Muhammad ya kuma yi godiya tare da jinjina ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu bisa irin Namijin kokarin da yake yi wajen tabbatar da ciyar da kasa gaba.

“Akwai tsare tsaren da shugaban ya Sanya a gaba a halin yanzu kamar shirin gaggawa na dokar ta baci a game da harkar Noma domin wadata kasa da abinci.

“Hakan ne ma yasa akwai wani take karkashin wannan Gwamnatin ta Bola Ahmed Tinubu domin kara inganta kasa baki daya da akewa lakabi da inganta harkokin tattalin arzikin kasa, Ilimi, Kiwon lafiya, inganta Noma da bayar da tallafin karatu karkashin bayar da bashin yin karatu mara ruwa da nufin samun ilimin da zai amfani kasa nan gaba da dai sauran aikace aikacen ci gaban kowa kamar yadda ya dace kuma yake a tsare a wannan Gwamnatin.

Kailani ya jaddada cewa domin a kara kyautatawa jama’ar kasa ” ana ganin kwanan nan za a bude rumbunan ajiyar abinci na Gwamnati domin a karya farashin Shinkafa, Gero, Dawa da sauran kayan abinci ta yadda talakawan kasa za su kara samun sauki, saboda haka ne muke yin kira ga daukacin jama’a da su kara hakuri domin gyara da da zafi amma bayan gyara dadi na nan tafe a kasa baki daya don haka muke kara ba jama’a hakuri duk abin da ake yi ana yo ne domin ci gaban kasa da al’ummarta baki daya.

” Ko batun cire tallafin nan da aka yi, ai ya dace jama’a su Sani cewa a can baya fa wadansu mutane ne yan tsiraru kawai ke kwasar kudin amma a yanzu gyara ya zo kuma nan gaba kadan kowa zai ji dadi ace gyara da aka cire tallafin domin abubuwa za su yi kyau, a saboda haka ne muke son yan Najeriya su marawa jam’iyya baya su kuma bayar da cikakken hadin kai ga Gwamnati domin ta samu sukunin aiwatar da ayyukan da ta Sanya a gaba na gyara da sake gina al’amuran kasa

About andiya

Check Also

Q1: More Nigerians buy Dangote Cement, as volume rises by 26.1% to 4.6MT 

  Strategies adopted by Dangote Cement to increase sales and ensure an adequate supply of …

Leave a Reply

Your email address will not be published.