Daga Imrana Abdullahi
Gwamnan Jihar Katsina Dokta Dikko Umar Radda, ya bayyana Samuwar ingantattun malamai a dukkan makarantu a ko’ina a matsayin sahihiyar hangar samar da ilimi mai inganci.
Gwamna Dikko Umar Radda ya bayyana hakan ne a cikin wata tattaunawar da ya yi da kafar yada labarai ta Talbijin mai suna “Channel” da kafar ta fara yadawa duniya a daren jiya Lahadi tare da yi wa jama’a alkawarin nuna tattaunawar a yau Litinin da karfe Tara na Dare.
Gwamna Radda ya ce koda za a samar da gini da kuma na’urar sanyaya Daki da dukkan kayan koyo da koyarwa, amma idan babu malamai masu inganci tamkar ba a yi komai ba ne domin ilimi baya samuwa sai da ingantattun malamai da za su Koyar.
“Saboda haka ne Dikko Radda ya tabbatarwa da duniya cewa sun dawo daga Rakiyar tsohon tsarin da ake amfani da shi a da can wajen daukar Malamai na rabawa jama’a wane ya kawo Kaza wane ya Kawo mutum kaza a dauki malaman makaranta, a wannan lokacin da muka dauki malaman makaranta sama da dubu Bakwai sai da muka gudanar da yin jarabawa ga wadanda za a dauka aikin malanta a Jihar Katsina.Kuma hatta da wakilan wadansu cibiyoyin kula da wannan aikin sun kasance a wurin kuma a gabansu aka yi sannan aka fitar da wannan lamba ta mutane sama da dubu Bakwai domin yin aikin koyarwa”.
Abin jira dai a gani shi ne idan Allah ya kai mu yau da karfe Tara na Dare suk masu hasken lantarki kuma suna da kudi a cikin na’urar tashoshin abin kallonsu ta dikoda za su kalli wannan tattaunawa da Gwamnan Jihar Katsina Dokta Dikko Umar Radda ya yi da kafar Talbijin ta “Channels”.