Home / KUNGIYOYI / Kakakin Majalisar Katsina Ya Zama Mataimakin Kungiyar Shugabannin Majalisar Dokoki Na Najeriya

Kakakin Majalisar Katsina Ya Zama Mataimakin Kungiyar Shugabannin Majalisar Dokoki Na Najeriya

Daga Imrana Abdullahi

Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Katsina, Alhaji Nasir Yahaya-Daura, ya zama sabon mataimakin shugaban kungiyar shugabannin majalisun dokokin Najeriya.

Babban Sakataren Yada Labarai na Majalisar, Malam Aminu Magaji, ne ya tabbatar da hakan a Katsina ranar Lahadi.

A cewarsa, hakan ya biyo bayan amincewar da masu neman tsayawa takara suka cimma na tsayawa takarar Yahaya-Daura bisa la’akari da irin hazakar da yake da shi a fannin shugabanci.

Ya ce an kuma zabi shugaban majalisar Katsina ne saboda dimbin gogewa da jajircewa da kuma daidaito wajen ciyar da majalisar dokokin Najeriya gaba.

Sanarwar da Magaji ya fitar ta kuma  ce zaben da ya gudana a Abuja ya kuma samu fitowar kakakin majalisar dokokin jihar Oyo Mista Adebo Ogundoyin a matsayin shugaban kungiyar shugabannin majalisun  dokokin na Jihohin Najeriya.

“Shugaban, mataimakinsa da sauran membobin zartarwa sun yi rantsuwar aiki nan take  bayan zaben,” in ji shi.

Ogundoyin dai ya zama shugaban taron ne biyo bayan janyewar kakakin majalisar dokokin jihar Ogun, Mista Taiwo Oluomo.

Kundin tsarin mulkin taron ya tanadi wa’adin mulki na shekaru biyu domin zababbun jami’an da za su rika karba-karba tsakanin yankin Arewaci da Kudancin kasar nan.

About andiya

Check Also

KASUPDA Organizes Stakeholders Engagement Programme

Community in the approved regularization layouts areas in Kaduna Metropolis have been advised to co- …

Leave a Reply

Your email address will not be published.