Related Articles
Gwamnan Jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana samun mutum na farko dauke da cutar Covid – 19 da ake kira da Korona bairos a Jihar.
Gwamnan ya bayyana hakan ne bayan da ya karbi rahoton kwamitin karta kwana da aka kafa a game da cutar korona a Jihar ya dai karbi rahoton ne a ranar Litinin a gidan Gwamnati da ke Sakkwato.
Tambuwal ya ce ” yaku yan uwana al’ummar Jihar Sakkwato ina son gaya maku cikin bacin rai da rashin jin dadi cewa an samu mutum na farko da yake dauke da cutar korona bairos a wannan Jihar ta Sakkwato”.
Kamar yadda ya bayyana wanda aka samu dauke da cutar yana asibitin koyarwa na jami’ar Ahmadu Bello yana karbar magani, saboda haka a yanzu da aka tabbatar da shi yana dauke da cutar za a mayar da shi zuwa cibiyar kwantar da masu dauke da cutar korona bairos ta Jihar Sakkwato da ke Amanawa.
Saboda haka ne ya yi kira ga daukacin al’ummar Jihar da su ci gaba da bayar da cikakken hadin kai da goyon baya ga matakan da ake dauka domin dakile cutar a Jihar baki daya
Tambuwal ya kara da bayanin cewa ” wannan lamari gaskiya ne irin yadda mule jin labarin wannan cutar to amma dai a yanzu ga abin nan a tare da mu don haka ya zama wajibi my kara kaimi a game da lamarin cutar Korona bairos domin yana yaduwara a tsakanin al’ummarmu baki daya.
” Ina kuma kara yin kira ga jama’a da su mutants dukkan matakan da ake dauka a game da wannan cuta saboda ana daukarsu ne domin kare lafiya da tattalin arziki tare da bunkasa harkokin kowa baki daya.
Gwamna Tambuwal ya kara ankarar da jama’a da su ci gaba da yin addu’o’in samun saukin wannan cuta ta Covid – 19