Home / Lafiya / Na Dauki Awa Biyu Ana Yin Taro Dani – El-Rufa’i

Na Dauki Awa Biyu Ana Yin Taro Dani – El-Rufa’i

Imrana Abdullahi
Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmad El-Rufa’i ya bayyana cewa ya dauki tsawon Awoyi biyu ana yin taron tattaunawa da shi daga wurin da yake a killace.
Gwamnan ya bayyana cewa taron da aka yi tare da shi daga inda yake a killace taro ne na kwamitin da aka kafa domin gudanar da aiki a kan batun kwayar cutar Covid – 19 da ake kira Korona kuma kwamitin na karkashin mataimakiyar Gwamnan Jihar ne Dakta Hadiza Balarabe.
Kasancewar akwai wadansu bayanan karya da suke yawo cewa wai ina wurin ajiye marasa lafiyar da halin da suke ciki ya yi tsanani a Legas saboda haka ga hotuna na nan domin Karyata bayanan karyar da ake kokarin rudar mutane da su.
Domin kawar da dukkan shakku, hakika na killace kaina tun tsawon kwanaki 24 a wani wuri a gidan Gwamnati, ina samun kulawar Likitoci a game da cutar Korona bairus kuma likitocin Gwamnatin Jihar kaduna daga ma’aikatar lafiyar Jihar ne ke duba ni.
Kamar yadda kuke gani a hoton nan ban yi aski ba tun da na killace kaina saboda Covid – 19 ina kuma fatar ganin lokacin da wannan cuta za ta zamo babu ita kwata kwata, kuma hakika ina fatar hakan da ikon Allah.
Hakika ina murna da farin cikin irin yadda wadannan jajirtattun ma’aikata ke aiki kuma ina mika godiya ga dukkan mutanen da suka nuna damuwa tare da tausayawa don haka ina tabbatarwa da jama’a cewa ina cikin koshin lafiya kuma ina samun ingantacciyar lafiya a kullum ranar duniya. Ina ma Allah godiya – Nasir @elrufai satan Afrilu 20,2020.

About andiya

Check Also

Tinubu Appoints Silas Ali Agara DG NDE

By Ibraheem Hamza Muhammad President Bola Ahmed Tinubu has approved the appointment of Honourable Silas …

Leave a Reply

Your email address will not be published.