Related Articles
…A fito a zabi dan takarar jam’iyyar Lebo- inji dan majalisa Ekene Abubakar Adam
Dan takarar majalisar Jihar Kaduna daga karamar hukumar Chikun Mista Solomon kenN take gaisawa da dimbin jama’ar da suka fito domin nuna Soyayyarsu gare shi a lokacin da yake Yakin neman jama’a domin zaben gobe Asabar da za a yi.
Dan majalisar wakilai ta tarayya karkashin jam’iyyar Lebo Ekene Abubakar Adam’s ya yi kira ga daukacin al’ummar karamar hukumar Chikun da su fito kwansu da kwarkwatarsu su zabi dan takarar majalisar Jihar Kaduna Solomon Adamu domin samun ingantaccen shugabanci a majalisar.
Dan majalisa Ekene Abubakar ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake zagayawa domin gangamin fadakar da jama’a muhimmancin zaben jam’iyyar Lebo musamman a karamar hukumar Chikun don ya wakilci jama’a a matakin majalisar jiha.