Home / Labarai / Muna Goyon Bayan Sanya Dokar Ta Baci A Zamfara – Abdullahi Ciroma

Muna Goyon Bayan Sanya Dokar Ta Baci A Zamfara – Abdullahi Ciroma

Wani dan kasuwa daga Jihar Kano Alhaji Abdullahi Yahaya Ciroma ya bayyana cikakken hadin kansa da goyon baya ga kokari da kiraye kirayen da wadansu mutane ke yi na a Sanya dokar ta baci da nufin inganta harkokin tsaron lafiya da dukiyar jama’a a Jihar Zamfara.
Abdullahi Yahaya Ciroma ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai a garin Kaduna.
A matsayina na musulmi kuma dan Arewa mai kishin Arewar da al’ummarta baki daya ya zama wajibi in nuna goyon baya da hadin kai ga shirin da kiraye kirayen da ake yi na a Sanya dokar ta baci saboda idan sojoji sun kama na tsawon watanni shida al’amuran za su inganta”.
Ciroma ya ci gaba da bayanin cewa ganin irin yadda lamarin yake a Jihar Zamfara ba zai yuwu ba haka kawai a zuba idanu abubuwan na faruwa.
Saboda haka ne muke yin kira ga Bola Ahmed Tinubu da ya duba sosai domin ba wata maganar siyasa muna ganin lallai Gwamna ba zai iya ba a gaskiya ba zai iya ba .
A game da batun cewa me ya sa suke ta maganar jihar Zamfara kawai kamar ba wata jiha sai ita kawai, sai Ciroma ya ce dalilin da ya sa hakan shi ne ” ka auna duk Jihohin haka suke? duk ba su zama a Jiharsu? Sannan abubuwa suna ta faruwa kusan kullum a Jihar Zamfara amma shin ya zauna a Jiharsa? Kullum ya na kasashen waje don haka ne muke yin kira ga Gwamnatin tarayya da ta yi kokarin duba lamarin masu yin Zanga zanga a Abuja wai a cire ministan kasa a ma’aikatar tsaro an dauki mutane an ba su kudi wai sai a cire minista Matawalle to, saboda Allah wannan wane irin hali ne, sai ka ce masu yin wasa ba dariya.
Sakamakon irin ayyukan da yake yi ne na ciyarwa kasa gaba muka ga ya dace kowa ya yaba masa tare da jinjina kuma ita Jihar abin da ya dace da ita shi ne dokar ta baci kawai.
“Idan kuma ana maganar shigi da fice ne wai domin a samawa Jiha wani abu, ai sai a gaya mana sau nawa gwamna ya kira yan jarida ya shaida masu irin ci gaban da aka samo a ficewa kasashen wajen da ake yi, ga wani ci gaban da aka samu ai ya kwashi yara an koya masu batun aikin tsaro na cikin al’umma shin sun yaki yan bindigar da ke damun Jihar Zamfara? lallai ya dace ya amsa wannan tambayar shin Jihar Katsina ba ta samar da irin wadannan masu sa kai na al’umma ba ana magana a kan hakan”.
Sakamakon hakan ne muke yin kira ga shugaban kasa da ya dub lamarin jihar Zamfara ayi abin da ya dace kawai.
” A matsayin mu na yan kasa ba zai yuwu ba mu zauna muna zura idanu ba haka kawai domin ai ba kowa ne zai iya gane abin da ke tafiya ba har kowa ya san abin da yake dai dai da wanda ba dai dai ba, kuma kamar yadda muke fadi ba maganar siyasa ba ce domin ai ba siyasa a batun kashe jama’a, mu musulmai ne ba wanda zai ce a bangaren musulmai ko na Kirista ana kashe mutane ba to ina maganar siyasa akwai siyasa ne a kashe mutane.
” Ni fa dan Kano ne amma saboda ina kishin Jihar Zamfara ina kishin Arewa ina kuma kishin Najeriya hakan ta Sanya ba zan zuba idanu ba ana yin abin da bai kamata ba ace in yi shuru”.
“Mai girma ministan kasa a ma’aikatar tsaro ai ko shi ma bai zauna ba yau idan aje wannan kasa gobe kuma ya na can waccan kasar ba wai ya zauna ba ne ko a kwanan baya a kasar Saudiyya da kasashe sama da Arba’in suka taru aka yi tattaunawa a kan harkar tsaro. Amma shi Gwamnan Zamfara a kan me yake yin tafiyar da yake yi ku yan jarida sai ku bincika  ku gano me yasa yake tafiyar da yake yi
A game da batun ko masu adawar nan suna zargi ne ko a kwai wani tabbaci sai Abdullahi Ciroma ya kada baki ya ce duk ba fa maganar yin zargi domin kowa ya san abin da ake ciki game da harkar yan bindiga a Zamfara, suna ta cin Karen su ba babbaka ba maganar zargi a ciki ko kadan a zahiri ne yan arewacin Najeriya sun Sani yan Najeriyar ma duk kowa ya Sani, shi yasa muke yin kira ga shugaban kasa da ya Sani cewa kuri’ar da aka bashi a Arewa lokacin biya fa ya yi don haka muna rokon alfarma ga shugaban kasa a dauki mataki idan nan gaba an saita Jihar shikenan.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.