Daga Imrana Abdullahi
Mataimakim darakta a tashar Jirgin ruwan kan Tudu da ke Kaduna kuma mai rikon tashar a yanzu Buba Danjuma ya bayana irin nasarar da suke samu a tashar da suke samun Kwantenar kaya dari biya (500) a wata.
Buba Danjuma ya bayyana wa manema labarai hakan ne a wajen taron da suka shiryawa masu ruwa da tsaki domin fadakarwa da ilmantarwa a game da irin yadda hukumar ke aiwatar da ayyukanta domin fadakarwa.
“Muna son gayawa yan kasuwa masu shigowa da kaya daga kasashen waje cewa tashar jirgin ruwan kan tudu ta Kaduna na kara bunkasa a kan ayyukan da suke gudanarwa kuma ana samun nasarori sosai don haka wannan kofa ce da kowa zai kawo kayansa tashar jirgin ruwa ta Kaduna daga ko ina a kasashen duniya a madadin mutum yaje Legas ya dauki kayansa da ya sayo daga kasadhen duniya kamar Amurka,Ingila, Jafar, Caina da dukkan kasashen duniya baki daya sai mutum yazo Kaduna ya dauki kayansa”.
Haka nan kuma idan mitum zai fitar da kaya kasashen waje kana da kasuwa a Ingila, Amurka ko Caina ko a kasar Dubai,sai mutum yazo Kaduna ya hada kayansa a kwantena za mu fadakar da mutum kan abin da ya dace ya yi domin ofishin hukumat na bude kuma dukkan sauran hukumomi da ma’aikatun gwamnati suna nan kakar hukumar NAFDAC, hukumar kula da ingantuwar kayayyaki ta SON, masu kula da fitar da kaya kasashen waje duk suna nan sai mutum ya zo a gaya masa ga abin da zai yi da wanda ba zai yi ba a gyara kaya a rufe su tsaf sai Caina, Indiya ko duk inda mutum zai kai kayansa a kasashen duniya baki daya, a kan haka ne muke gaya wa jama’a cewa gwamnatin Kaduna ma da ta tarayya da ma’aikayar kula da shigowa da kaya ko fitar da su kasashen waje da kuma tashar jirgin ruwa sune suka assasa wannan tashar aka samar da wannan tashar”.
Manufar wannan samar da tashar shi ne domin a samar da ci gaba kusa da jama’a har kofat gida shi ya sa aka ce tashar ta zama a nan saboda haka ana kira ga yaya cewa kowa ya shiga wanann kasuwancin fitar da kaya kasasjen waje da zai katgaga samar da kudin shiga tare da samar da ayyukan yi har tattalin arzikin kasa ya samu karfi kuma idan an ci gaba da harkar fitar da kaya lallai Naira ta Najeriya za ta yi karfi.
“Duk da halin da ake ciki kamar yadfa aka ce jirgin kasa ne zai rika kawo mana kaya saboda idan jirgin kasa na safarar kaya ba za a samu jetin gwano ko tsaiko da sauransu idan jirgim ya taso daga can kao tsaye zai zo tashar mu ta kan tudu. Amma saboda rashin zuwan jirgin a yanzu muna yin amfani da motocin tirela ne shi ya sa kake ganin ana samun tsada domin wahalar da ke ciki duk da haka ana samin sauki don haka a yanzu muna samun Kwantenoni dari biyar na sauka a tashar jirgin ruwa ta kan tudu da ke Kaduna a yanzu haka ana samimsu a tashar Kaduna a waya daya. Amma idan ace akwai jirgon kasa hakika Allah ne kawai ya san irin yawan kayan da za a samu ba tare da ana je Legas ko wani wuri ba yan kasuwa za su samu sauki kuma jama’ar mu za su samu aikim yi sosai aikin na da yawa ba zai lisaafu ba akwai ayyukan dako,Sufuri,kiliyarans,da dai sauran su da yawa don haka muke yin kira ga mutane su shigo wannan hatkar don kowa ya sami karfin da ya dace”.
“A yanzu mun fara yin magana da Gwamnatin jihar Kaduna da a ba wannan tashar damar shiga da kaya a koda yaushe ta yadda za a daina samun matsalar shiga da fita na tireloli, mima son tireless ta shigo ta sauke kaya ba tare da samun wata matsala ba domin suna kawo dukiya ne a kasa don haka a bayar da taomakon da ya kamata ba tare da wata tsangwama ba su shiga su fita”, inji buba Danjuma mataimakin datakta mai rikon tashar jirgin riwa ta kan tudu da ke Kaduna.