….Jihar Zamfara Na Bukatar Addu’a Ne domin Jihar Na Cikin wani Ciwo
Alhaji Bashir Nafaru Talatar Mafara, Dan takarar ne da ya tsayawa jam’iyyar ADC takarar Dan majalisar tarayya a zaben da ya gabata a 2023, kuma Dan takarar majalisar tarayya a halin yanzu a jam’iyyar ADC a shekarar 2027 Mai zuwa in Allah ya yarda, ya bayyana halin da Ake ciki a jihar Zamfara a matsayin wani Abu da ya zamarwa al’umma wani Babban ciwon da BA a San inda za a je BA domin samo maganinsa.
Ya bayyana hakan ne a lokacin da Yake tattaunawa da wakilin mu inda ya ce hakika harkar sai dai ace Innalillahi wa’inna alaihirraji’un kawai.
“Abun bakin ciki da Ban haushi abin da za a yi abin da yakamata a hada Kai tsakanin Iyaye, Kakanni, Yayye da Kanne a harkar Siyasa a tunkari abin da yakamata Amma a halin yanzu BA Shi ne a gaban iyayen Siyasar BA KO Kada a.
Bashir Nafaru, Ya ci gaba da bayanin cewa a yanzu har ta Kai a Jihar Zamfara mutum daya NE ya tsokane masu idanu kuma BA Shi yakamata a duba BA domin mu a iya ganinmu Shi ne abin da yakamata a duba Shi ne meye matsalar Jihar Zamfara me Jihar ke bukatar kuma me yakamata ayi Mata.
Sai ya yi zargin cewa a matsayin jam’iyyar APC a yanzu BA abin da ke cikin ta sai harkar bakin ciki zalla kawai jam’iyyar APC ta Kai inda take bukatar Yan Zamfara su Kai domin a yanzu duk Wanda Bai iya yin harkar munafunci ba BA zai iya yin APC BA, APC ta dawo da wasu Yan a fasa kowa ya rasa da suka kasance batagari da ke kawo WA Jihar matsala a lokacin zaben 2023 da ya gabata. Wanda Allah ya kaddara aka Bashi matsayin minista na tsaro da yakasance Dan asalin karamar hukumar Maradun sannan kuma ya dade ya na bautawa al’umma ya na yin Siyasa tun daga bakin PDP har inda Allah ya kaddara ya dawo APC, Amma abin bauhaushi irin su Marafan Gusau irinsu Dokta Sani Shinkafi babu abin takaici kamar yadda suke fitowa duk da irin yadda suka amfana da Matawalle a lokacin da ya na Gwamna har a yanzu da Yake ministan tsaro duk matsalar da ta tinkare su ta same su ta Kudi CE don haka yakamata a rika yin abubuwa da tunani kuma ni a matsayina na Dan jam’iyyar ADC ina nan a cikin ta Amma a duk shugabannin nan Wallahi Dauda Ya fi su.
“Dauda sai dai ace ya dauko mutanen da BA Yan Jihar Zamfara ba suna amfana da kudin Jihar Zamfara don haka muke Fadakar da Jama’a cewa da a dauko wadanda za su yi wa Jihar Zamfara aiki su samu abin duniya su ta fi su amfanar da Yan uwansu da a bar mana Yan bakin ciki kuma fa domin APC Wallahi maganar bakin ciki CE zalla kawai. Bai yuwuwa ace mutum guda daya kawaii kuke bakin ciki nai don kawai Allah ya yi Shi Dan majalisa Allah ya yi Shi Kwamishina Matawalle Allah ya yi Shi Gwamna Allah ya yi Shi minista don haka mu BA jayayya muke bukata a jihar Zamfara ba A’a WA zai kawo mana ci gaba kawai Abar Yan Zamfara da halinsu da abin da ya sha masu Kai Abar Yan Zamfara da halin da muke Ciki Yan Zamfara addu’a kawai suke Nema Allah ya sa jama’ar mu su gano a bar yi wa Yan uwanmu sharri duk Wanda ke Zamfara Dan uwan Juna ne.
“Marafa ya sani cewa fa mu muna cikin yaran Ka kuma Gwamna Ka Nema Kai Ka ba ta Siyasar Zamfara, mu muna cikin yaran Ka”.
“Kai kuma Dokta Sani Abdullahi Shinkafi Dan Siyasar Kasuwa kake inda ace BA Dan Siyasar Kasuwa kake BA kuma kwadayi gareka ai da yanzu Kai ma Ka rika Jihar Zamfara tun da Ka fito a matsayin Ka na Dan takarar gwamnan Jihar Zamfara kuma tsohon Sakataren jam’iyyar APGA na kasa babu Wanda ya yi karfinka lokacin Amma saboda kwadayi da Ka ji Kudi sai kawai kake Ka Tara Yan midiya duk Dan takarar da kake tsayarwa babu Wanda Ka Bashi satifiket ni ina Zamfara na San Yan Zamfara kuma ni na San mutanenka da kake tsayarwa duk yara ne kake tsayarwa a zo daga karshe Ka sayar da su Baki daya Ka rika ba su Kudi daga mai dubu ashirin, Talatin sai Mai dubu Hamsin, Bashir Nafaru Ya yi zargin, don haka mun San komai fa
THESHIELD Garkuwa