Shugaban Karamar Hukumar Funtua, Alhaji Abdulmutallab Jibrin Sulaiman Goya, ya bayyana jin daɗinsa tare da yabawa Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda, PhD, CON, bisa jajircewar sa na kafa cibiyar koyon sana’o’in hannu a karamar hukumar Funtua.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata takardar sanarwa Mai dauke da SA hannun
Bashir Yero,Jami’in Watsa Labarai na Karamar Hukumar Funtua a Jihar Katsina, inda sanarwar ta ce.
Alhaji Goya ya yi wannan yabo ne a yayin bikin kaddamar da fara horaswa da kuma bude cibiyar koyon sana’o’in wadda za ta taimaka wajen ba matasa Maza da Mata kwarewa domin dogaro da kai.
Sana’o’in da za a koyar a cibiyar sun haɗa da:
Sana’ar dinki
Kwalliya wadda ta kunshi (sabulu, man shafawa, gyaran gashi na maza da mata)
Koyon aikin sa wuta mai amfani da hasken rana (solar installation)
Koyon girke-girke
Sana’ar yin jaka da takalma (leather work)
Shugaban karamar hukumar ya bayyana cewa irin wadannan cibiyoyi guda hudu ne kawai ake da su a fadin jihar Katsina, wadanda suke a Funtua, Batagarawa, Jibiya da kuma Mai’aduwa sai ya janyo hankalin daliban da za su amfana da su dage wajen karatu da aiwatar da dukkan darussa domin su samu ingantacciyar kwarewa da za ta basu damar dogaro da kawunan su.
Ya ce an samar da cibiyoyin ne ta hadin gwiwa tsakanin gwamnatin Jamani da Centre for Community Development and Research Network (CCDRN) da kuma Gwamnatin Jihar Katsina.
Alhaji Goya ya kara da cewa dukkan kwasa-kwasan da ake koyarwa an wadata su da kayan aiki na zamani. Haka kuma ya yi alkawarin ba wa mahalarta jari bayan kammala horo, tare da ci gaba da biyansu kudin sufuri har tsawon lokacin da za a kammala horaswar.
A nasa bangaren, Koodinetan shirin, Malam Abubakar Tukur, ya bayyana cewa horon zai dauki tsawon watanni shida, sannan a yaye daliban, a kuma dauki sabon rukuni. Ya ce shirin zai ci gaba har zuwa shekaru hudu nan gaba. A wannan zangon dai, matasa Maza da Mata 130 daga Mazabun Maska, Dukke da Makera ne suka sami damar shiga cikin shirin.
A jawaban su Shugaban Kwamitin Gudanarwa na Cibiyar, Mai Unguwa Abubakar Sani; Community Development Officer (CDO)Malam Ibrahim Ibrahim Kusada; da Manajar Cibiyar, Hajiya Binta Mustafa, sun gode wa Shugaban Karamar Hukumar Funtua da Gwamnan Jihar Katsina saboda samar da wannan muhimmiya cibiyar. Sun kuma bayar da tabbacin cewa za su kula da tsari da ingancin horaswar domin tabbatar da cimma burin shirin.
THESHIELD Garkuwa