…Adalci muke bukatar ayi mana
Daga Imrana Abdullahi
Daukacin yan takarar kujerun majalisar dattawa da kuma wasu daga cikin yan takarar majalisar wakilai karkashin jam’iyyar APC sun bukaci shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya sanya baki a game da irin yadda ake gudanar da zaben fitar da yan takarar majalisun daitawa da na wakilai a jihar Kaduna.
A wajen wani babban taron manema labarai da suka yi a cibiyar yan jaridu ta kasa reshen jihar Kaduna xaukacin yan takarar neman kujerar majalisar dattawa karkashin jam’iyyar APC sun koma da matsalar rashin adalcin da suke cewa an yi masu na rashin yin komai da su game da zaben fitar da gwanin kamar yadda dokar jam’iyya ta tanadar.
Yan takarar sun ce duk da sun fi kowa a cikin jam’iyyar jarin yi wa jam’iyyar wahala tun ba yau ba, amma sai ga shi a yanzu a matsayinsu na yan takarar da suka yi wa APC wahala a Mazabu da garuruwansu ana yi masu wariya.
“Muna zargin Gwamnan Jihar Kaduna Sanata Uba Sani da haifar da wannan matsalar ta nunawa wadansu yan takarar majalisar wakilai da kuma tarayya wariya, saboda a halin yanzu ba mu san inda wadanda za su gudanar da wannan zaben suke ba kuma ba mu ga kayan zaben ba ba wanda zai gaya maka wuri ko inda za a yi zaben, sai dai sun je suna yin zargin Gwamnan Jihar Kaduna da boye wadanda za su gudanar da zaben fitar da yan takara a Gobe Litinin domin sanin yan takarar da za su tsayawa APC takarar majalisar dokoki a dukkan shiyyoyi Uku da ake da su a fadin Jihar Kaduna baki daya.
Sun ce su a iya saninsu ba wanda ya janye daga cikin wannan yunkurin ayi masu adalci kamar yadda dokar kasa ta tanadar
“Mun yi taron tattaunawa a cikin daren jiya har karfe hudu na asuba kuma duk mun yi tare da kowa sai dai muna kan hanyar zuwa wannan wurin taron manema labarai na yanzu sai Shettima Yerima yake shaida mana cewa zai janye takararsa bayan mun kammala rubuta abin da za mu shaidawa manema labarai duk da ya ce ya na tare da mu”, inji yan takara.
Sai dai a karshe sun ce za su bi dokar kasa a wajen tabbatar da bin hakkinsu kamar yadda dokar kasa ta tanadar.
Sun kuma ce sun aikewa dukkan hukumomin tsaro da shugaba Bola Ahmed Tinubu da wannan koken na su.
Takardar koken na dauke da suka karantawa manema labarai na dauke da sa hannun tsohon Sanata kuma ɗan takara a halin yanzu karkashin APC Sanata Danjuma LAAH, daga kudancin Kaduna da ya sanya hannu a takardar a ranar 17 ga wannan wata
Sai tsohon dan majalisar wakilai tsawon shekaru Takwas kuma ɗan takarar kujerar Sanata a yanzu Honarabul Yusuf Bala Ikara,daga shiyya ta daya
Sai kuma ɗan takara Michael Ayuba Aura, da yake takara daga yankin Kudancin kaduna.
Kuma takardar na dauke da sunayen wadansu mutane Goma sha daya da ke yin takarar majalisar wakilai da kuma yin takarar majalisar dattawa duk suna yin korafinsu game da ayi masu adalci ba Magudi ba.
“Mun bayar da awoyi 24 idan babu wani abu muhimmin da aka yi lallai ba shakka za mu ta fi kotu domin neman hakkin mu, domin ba gudu ba ja da baya”, inji yan takarar na APC a jihar Kaduna.
THESHIELD Garkuwa