…Ni Ba Zan Ci Amanar ku Ba, inji Yusuf Bala
Daga Imrana Abdullahi
Homarabul Yusuf Bala Ikara da ke neman jam’iyyar APC ta tsayar da shi takarar neman kujerar dan majalisar dattawan Najeriya domin wakiltar Mazabar shiyya ta daya mai dauke da kananan hukumomi Takwas (8) ya kaddamar da takararsa a garin Zariya hedikwatar shiyyar.
Yusuf Bala Ikara ya shaidawa dimbin al’ummar da suka taru a wajen taron cewa babban abin da suke neman daga wurin jam’iyyar APC shi ne adalci ko dai ayi Sasanci a barwa mutanen karkara su yi takara ko kuma ayi zabe wannan shi ne kawai abin da mutanen karkara ke bukata ba kari ba ragi.
“Na San aikin saboda na yi dan majalisar wakilai ta tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Ikara da Kubau a majalisar wakilai na tsawon shekaru Takwas, don haka na san aikin ba wata tantama a kan wannan, hakika ina tabbatarwa da kowa cewa na cancanta in zama dan majalisar dattawa domin in wakilci mutanen shiyya ta daya”.
“Kun san mu mutanen karkara kawuna guda biyu muke da shi akwai kan yin Dako Akwai kuma na yin bari don haka lallai ya dace a san hakan a koda yaushe”.
Dan takarar ya kuma dauki alkawarin cewa a gaban dimbin jama’ar da suka taru cewa su sani da shi ba zai ci al’amar su ba a koda yaushe a kowane irin hali aka shiga.
Sai ya kara yin kira ga daukacin ya’yan jam’iyyar APC da kowa ya koma gida a bi jama’a lungu da sako a fadakar da su cewa su tabbatar da su. Yi katin zama dan jam’iyyar APC da ake yi a halin yanzu, domin sai da shi ne kawai mutum zai iya yin zaben fitar da Gwani wato dan takarar da za a fitar ya tsayawa jam’iyya domin karawa da sauran yan takarar na wasu jam’iyyu.
Sai ya tabbatarwa da ya’yan jam’iyyar cewa za a yi zaben ne a kowace hedikwatar mazaba da ke karamar hukuma ta hanyar Alhaji bayan Alhaji kuma Hajiya bayan Hajiya bayan an tabbatar da mutum ya na da katin shaidar zama dan jam’iyya.
“Mu ga ba wai muna yi wa Gwamnatin Jihar Tawaye ba ne kuma suna girmama Gwamnan Jihar Kaduna matuka a matsayinsa na Uban kowa a jihar Kaduna da jam’iyyar APC, Amma abin da kowa yake nema shi ne ayi wa jama’ar karkara adalci wajen fitar da yan takara”.
“Yankin shiyyar ta daya fa a sani a nan ne kuri’a zalla take domin duk yankin shiyya ta daya ya fi kowa ne yanki bayar da kuri’a a koda yaushe a duk lokacin da aka gudanar da zabe ,wannan magana ba ko shakka ballantana ayi wata tantama a kan zancen”.
Kananan hukumomin da suka hadu suka yi wannan shiyya ta daya sun hada da Zariya,Sabon Gari, Kubau,Ikara,Soba, Lere, Kudan da Makarfi.
Daukacin wadanda suka halarci taron sun bayyana ra’ayinsu ta hanyar yin kira ga Gwamnatin Jihar Kaduna karkashin jagorancin Sanata Uba Sani da cewa suna bukatar ayi wa jama’ar karkara adalci.
Wadanda suka halarci taron sun hada da manyan yan siyasar jam’iyyar APC da manyan yan kasuwar da suka fito daga yankin karkara a wannan shiyyar da kuma tsofaffin manyan ma’aikata da suka yi ritaya daga manya manyan ayyukan gwamnati duk sun yi karkara a wannan taro a garin Zariya sun kuma ce ayi wa al’ummar karkara adalci a wannan karon.
THESHIELD Garkuwa