Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya kafa sabon tarihi bayan da aka gudanar da jigilar farko na aikin Hajji daga Filin Jirgin Sama na Ƙasa da Ƙasa da ke Gusau.
Jirgin Hajjin na farko ya tashi ne daga filin jirgin ranar Juma’a ɗauke da maniyyata 415 na jihar Zamfara a jirgin kamfanin Max Air mai lamba NGL270 zuwa ƙasar Saudiyya domin gudanar da aikin Hajjin bana.
Rahotanni sun nuna cewa daga cikin maniyyatan akwai maza 288 da mata 127.
Da yake jawabi yayin ƙaddamar da tashin jirgin, Gwamna Lawal ya bayyana farin cikin sa da godiyar sa bisa ganin wannan gagarumin ci gaba da ya ce zai kasance abin tarihi a jihar Zamfara.
Gwamnan ya bayyana gina Filin Jirgin Sama na Ƙasa da Ƙasa na Gusau a matsayin ɗaya daga cikin manyan ayyukan tarihi da gwamnatin sa ta sa a gaba, kuma alhamdu lillahi, ta cimma nasara.
“Ina farin ciki matuƙa a yau ganin maniyyatan mu suna tashi kai tsaye daga Filin Jirgin Sama na Gusau zuwa ƙasar Saudiyya domin aikin Hajjin bana,” in ji gwamnan.
Ya ƙara da cewa, mutane da dama sun yi shakku kan yiwuwar aikin ya zama gaskiya, amma yanzu an tabbatar da hakan bayan an fara aikin gina filin jirgin tun ranar 18 ga watan Yunin 2024.
“Ba zan iya bayyana irin farin cikin da nake ciki ba. Wannan babbar dama ce ga maniyyatanmu domin tafiya cikin sauƙi da kwanciyar hankali. Cikin ƙasa da awa huɗu za su isa Saudiyya. A baya kuwa sai sun je Kano ko Sakkwato kafin su samu jirgin Hajji,” in ji gwamnan.
Gwamnan ya ce, wannan nasara wani babban mataki ne na tarihi tare da cika ɗaya daga cikin alƙawuran da ya ɗauka a lokacin yaƙin neman zaɓe.
“Wannan tarihi ne mai girma kuma cikar alƙawarin da muka yi wa al’umma. Ina da ƙudurin ci gaba da aiwatar da ayyukan ci gaba domin jihar mu,” in ji shi.
Ya gode wa al’ummar jihar bisa addu’o’insu da kuma amincewar da suka nuna ga gwamnatinsa, yana mai cewa wannan shi ne farkon wasu manyan nasarori.
Haka kuma gwamnan ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta fara tattaunawa da kamfanonin jiragen sama domin fara zirga-zirgar kasuwanci daga Filin Jirgin Sama na Gusau nan gaba.
A ƙarshe, ya yi wa maniyyatan fatan sauka lafiya da gudanar da Hajji cikin nasara, tare da roƙon su da su yi addu’a ga jihar Zamfara da ma Nijeriya baki ɗaya.
Sanarwar ta fito ne ta hannun mai magana da yawun gwamnan jihar Zamfara, SULAIMAN BALA IDRIS.
THESHIELD Garkuwa