Home / Labarai / Auren Mata Da Yawa Ne Ke Jawo Mana Talauci A Arewa – Sarki Sanusi

Auren Mata Da Yawa Ne Ke Jawo Mana Talauci A Arewa – Sarki Sanusi

Sarkin Kano, Muhammad Sanusi na II, ya bayyana cewa matukar mutanen yankin Arewa ba su canja al’adunsu ba to za su ci gaba da zama a cikin bakin talauci ne da ci baya.
Sarkin ya yi wannan maganar ne a garin Gusau, babban birnin jihar Zamfara, a lokacin da ya halarci taron kaddamar da wata takarda da aka sanyawa suna ”Gudummawar makarantun jami’a wajen ci gaban kasa’, wanda Dr Usman Bugaji ya gabatar a jami’ar tarayya ta garin Gusau a jiya Juma’a.
Sarkin ya bayyana cewa al’adar Hausa ta auren mace fiye da daya, bayan dayar ma ba iya daukar dawainiyar ta suke yi ba, shi ne babban musabbabin da ya sanya yankin arewa zai ci gaba da zama a cikin rashin ci gaba da talauci.
Ya ce: “Akwai mutanen da basa iya ciyar da mace daya ma, amma sai kaga sunje sun karo mata uku, sannan suyi ta haifar yaran da baza su iya daukar nauyinsu ba.”
Ya ce har sai mun canja wannan al’adar ta mu tukunna yankin arewa zai samu cigaba.
A cewar shi, “Yankin arewa na da kashi 80 na talauci, kudu kuma suna da kashi 20, saboda kawai mun dauki al’adar auren mata da yawa da haifar yaran da baza mu iya daukar nauyinsu ba, a karshe sai dai mu bar su suna bara a tituna.”
Ya kara da cewa wasu mazajen za su saki matansu, su tare yara masu yawan gaske, matan ne za su cigaba da daukar nauyinsu, Sarkin ya ce wannan kawai na daya daga cikin dalilan da ya sanya muke samun ‘yan ta’adda a yankin mu.
“Matsalar shaye-shaye, Boko Haram, ta’addanci da rashin aikin yi da muke fama dasu a yanzu, ba komai bane akan abinda zai zo mana nan da shekara 20 zuwa 30,” inji shi.
Ya bukaci jami’o’in Najeriya da su fito da wata hanya da za ta kawo karshen wannan al’ada ta mu.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.