Home / Labarai / Yadda Aka Sace Ni Da Yi Mini Fade – Halima Abdullahi

Yadda Aka Sace Ni Da Yi Mini Fade – Halima Abdullahi

Yadda Aka Sace Ni Da Yi Mini Fade – Halima Abdullahi
Halima Abdullahi, wata budurwa ne mai shekaru 18 da ke Aji uku na babbar makarantar sakandare  yar asalin karamar hukumar kankara da ke cikin Jihar Katsina ta bayyana irin yadda aka ci zarafinta lokacin da masu garkuwa da mutane suka sace ta
Halima Abdullahi ta bayyana cewa a lokacin da take hannun masu garkuwa da mutanen sun ci zarafinta ta hanyar kwar da budurcinta a tsawon sama da sati daya da ta yi a wurinsu.
Duk da haka sun karbi makudan kudin fansa bayan sun gama yin lalata da ita, Lamar dai yadda bayanai suka tabbatar.
An dai sace Halima ne a ranar 15 ga watan Janairu, 2020 da misalin karfe 8:00 na Yamma. Kamar yadda ta ce tana cikin tafiya ne a gefen Titi, lokacin da mutanen da bata san ko suwaye ba suka kamata suka saka cikin motarsu. Bayan sun tilastata da karfin tsiya sai nan take suka daure  mata idanunta suka kuma fesa mata wata Hoda nan take hankalinta ya gushe bata san inda take ba. A lokacin da hankalinta ya dawo sai kawai ta ganta zagaye da mutane a wani wurin da bata sani ba.
Sai kawai nan take suka ce ta kira mahaifinta ta kuma gaya masa ya biya kudi naira miliyan daya da rabi in kuma ba haka ba za su kashe ta in har sun ki aikata hakan. Bayan ta kira shi ya yi alkawarin zai kai masu kudin kuma nan take ya rokesu da kada su taba ta ganin cewa ita yarinya ce. Sun dauki kwarai uku kafin su hada wadannan kudin su biya fansar Halima da yan ta adda suka kama.
A wannan lokacin da ta zauna a wurin masu garkuwa da mutanen ne shugabansu ya yi zina da ita da karfin tsiya duk da rokonsa da aka yi da kada ya kawar mata da budurcinta amma sai da ya aikata muguwar manufarsa.
Sun dai sako Halima ne a ranar 22 ga watan Janairu, 2020 sati daya bayan sun sace ta an kuma dauke ta zuwa babban asibitin Kankara domin duba tafiyarta da kuma sauran Gwaje gwaje.
Jami’an tsaron da ke wurin sun bayyana cewa suna yin bakin kokarin domin magance matsalar tsaron da ke addabar yankin, sun yi alkawarin gano inda suke tare da kamasu yan ta’addan.

About andiya

Check Also

Dangote crashes Diesel price to N1,000 per litre

In an unprecedented move, Dangote Petroleum Refinery has announced a further reduction of the price of diesel from …

Leave a Reply

Your email address will not be published.