Related Articles
Imrana Abdullahi
Alhaji Muhammad Sani Dattijo, shugaban ma’aikatan gidan Gwamnatin Jihar Kaduna ne ya bayyana cewa Gwamnatin da Malam Nasiru Ahmad El- Rufa’i ke yi wa jagoranci za ta gina tituna masu tsawon kilomita 10 a kowace karamar hukuma kamar yadda aka yi a karamar hukumar Kachiya a halin yanzu.
Muhammad Sani Dattijo ya bayyana hakan ne a lokacin da yake tattaunawa da gidan rediyon tarayya Kaduna, inda ya ce dukkan titunan da Gwamnatin Malam Nasiru Ahmad El-Rufa’I, ke aiwatarwa za su kammala su baki daya.
Ya lissafa wurare inda Gwamnatin ke aiwatar da aikin titin da suka hada da titin kwalejin yan Sanda zuwa Almannar ya hade da titin Tafawa Balewa sai titin Katuru, Muhammadu Buhari Way da layin Alkali da a yanzu ankammala wasu tuni jama’a na amfani da Tagwayen hanya a cikin kaduna ga kuma aikin Gadar Kawo da ta kasuwa da ta hada da sabon tagwayen hanyar da aka yi a titin Yakubu Gowon a cikin garin Kaduna.
Ga aikin mahadar titi Sakkwato kusa da ofishin KASTLEA KASTLEA aikin titi a unguwar Barnawa da sauran wadansu wurare da Gwamnati ke mayar da tituna Tagwaye domin dimbin jama’a marasa iyaka su amfana dare da rana.
“Kowace karamar hukuma za ta samu tituna masu tsawon kilomita 10 Karin Gwamnatin ta kare lokacinta
Ya kuma bayyana cewa za a mayar da titin Katuru ya zama Otal Otal ne a wurin saboda duk bakon da yazo kawai kai tsaye ya san wurin da zai je.
Akwai aikin Dam da za a yi domin wanda ake da shi ya yi wa jama’a kadan duk da cewa aikin Dam na daukar lokaci mai tsawo amma dai ba shakka Gwamnatin Malam za ta fara wannan aikin.