Related Articles
Wannan lamarin dai ya faru ne a ranar Asabar da misalin karfe 9 na Yamma a wurin gidajen masu aiki a makarantar.
Mahaifin Yaran da aka dauke a halin yanzu yana asibitin koyarwa na jami’ar Ahmadu Bello da ke Shika Zariya ana duba lafiyarsa sakamakon irin raunukan da ya samu daga harbin Bindiga
Baki dayan Malamin makarantar da kuma ma’aikacin da ba Malami ba makwabta ne da ke a layin Aliyu unguwar Tudun Wada Zariya.
Jami’in da ke hulda da jama’a a rundunar Yan Sanda ta kasa a Jihar Kaduna ASP Muhammad Jalige ya tabbatar da faruwar abin da ya faru a makarantar Nuhu Bamalli.
Ya ce tuni aka fara gudanar da bincike a kan lamarin domin a kubutar da wadanda aka kwashe.
Ya shawarci mazauna wannan makaranta da su ci gaba da zama cikin natsuwa musamman ganin ana ta kokarin samo inda mutanen da aka kwashe suke domin kubutar da su.