Home / Labarai / Gwamna Zullum Ya Bankado Ma’aikatan Bogi Dubu 22, 556

Gwamna Zullum Ya Bankado Ma’aikatan Bogi Dubu 22, 556

Gwamna Zullum Ya Bankado Ma’aikatan Bogi Dubu 22, 556

Mustapha Imrana Abdullahi
A kokarin Gwamnan Jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum na ganin an tsaftace jadawalin biyan Albashi daga yan Bogi masu karbar dimbin albashin jama’a da sunan yi wa Jihar aiki a halin yanzu Gwamnatinsa ta bankaɗo malaman bogi da ma’aikatan ƙananan hukumomin dake jihar kimanin 22,556 a wani yunkurin tantance ma’aikata da malamai da Gwamnatin jihar ta bayar da umarnin aiwatarwa.

Alƙaluman sun nuna kimanin ma’aikatan bogi 14,662 aka gano a ƙananan hukumomin jihar yayin da aka gano wasu malaman karya har 7,794 a ɓangaren ilimi.

 

Da ya ke gabatar da rahoton, shugaban kwamitin tantance malaman firamare, Dr. Shettima Kullima, ya ce, tantancewar ta samarwa jihar rarar kuɗi sama da miliyan 183 da suke zurarewa a iya ɓangaren malaman firamare kaɗai dake ƙananan hukumar 27 dake faɗin jihar.

 

Bayan karɓar rahoton ne kuma gwamna Zulum, ya bayyana cewa ya dauki wannan mataki ne don inganta harkar ilimi a jihar Borno, kasancewar gwamnatinsa ta baiwa harkar ilimin firamare fifiko.

 

An fara tantance ma’aikata a jihar ta Borno tun a shekarar 2013 inda aka samo dubbanin ma’aikatan bogi. Gwamna Zulum ne ya yanke shawarar faɗaɗa tantancewar har zuwa ma’aikatan ƙananan hukumomin jihar Borno guda ashirin da bakwai.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.