Related Articles
Allah Ya Yi Wa Wakilin VOA Rasuwa
Mustapha Imrana Abdullahi
Kungiyar yan jarida ta kasa (NUJ) reshen Jihar Adamawa ta bayyana kaduwarta da samun labarin rasuwar daya daga cikin yayanta wakilin Muryar Amurka, Ibrahim Abdul’Aziz.
Tsohon dan jarida wanda kafin rasuwarsa wakili ne na gidan rediyon muryar Amurka (VOA) kuma mawallafin jaridar “Adamawa Times” ya rasu ne sakamakon hadarin motar da ya rutsa da shi a yau Juma’a a kan hanyar Gombe zuwa Alkaleri lokacin da yaje yin wani aiki.
Ibrahim Abdul’Aziz dai kasancewarsa tsohon dan jarida ya yi aiki da kafafen yada labarai da dama daga ciki har da jaridar daily trust da kuma gidan rediyon Nagarta da ke Kaduna.
Kamar yadda sanarwar da kungiyar NUJ ta kasa reshen Jihar Adamawa mai dauke da sa hannun sakataren Jihar Fidelis Jockthan, ta sanar cewa a gobe ne za a yi ma marigayi Abdul’Aziz Sallah idan Allah ya kaimu lafiya.