Home / Lafiya / Muna Yaba Wa Gwamnatin Tarayya Bisa Inganta Asibitoci – Farfesa Jika

Muna Yaba Wa Gwamnatin Tarayya Bisa Inganta Asibitoci – Farfesa Jika

Muna Yaba Wa Gwamnatin Tarayya Bisa Inganta Asibitoci – Farfesa Jika
Mustapha Imrana Abdullahi
Shugaban da ke kula da babban asibitin masu fama da matsalar kwakwalwa na Gwamnatin tarayya Farfesa Abdulkareem Jika Yusuf, ya bayyana farin cikinsa da jin dadinsa da halin da asibitin yake ciki sakamakon samun aikace aikacen bunkasa babban asibitin domin amfanin jama’a.
Farfesa Abdulkareem Jika Yusuf, ya dai bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai a Kaduna, jim kadan bayan an kammala zagayawa da su domin ganin irin yadda aikin ci gaba yake gudana a daukacin harabar asibitin.
Kamar yadda Farfesan ya shaidawa manema labaran bayan sun ganewa idanunsu irin yadda ayyuka ke gudana ya bayyana cewa a halin yanzu Gwamnati ta kara wuraren kula da lafiyar jama’a da a can baya babu su.
“Kamar irin wurin wankin Koda, babban wurin Gwaje gwajen gano cututtukan da ka iya samuwa ko nan gaba da ba a sansu ba da kuma wurin ajiye masu dauke da cutar Korona da cututtuka makamantan hakan, duk yanzu ga su an samar da su a dan kankanin lokaci”, Inji Jika Yusuf.
Kamar dai yadda aka zagaya da manema labaran mun ganewa idanun mu sababbin Injunan zamani masu inganci kirar kasar Italiya huda hudu (4) domin wankin Koda ga masu fama da matsalar ciwon Koda, kuma ana yin amfani da du wajen duba yanayin jinin jikin mutum.
Sannan mara lafiya za iya yin amfani da Gado ko kuma ya zauna a kan kujera da wata na’ura a hannunsa, ya kwanta ko ya dan kishingida idan ana yi masa wankin Kodar, Sannan babu maganar dauke wuta domin akwai manya manyan na’urorin da za su ajiye hasken wutar lantarki tsawon lokaci idan ayi ta amfani da Injunan wankin Kodar, kamar yadda wani babban jami’in kamfanin SUDABELT da ke aikin Sanya Gadaje, Injunan zamani ya shaidawa manema labarai lokacin da suka kai wannan ziyarar domin ganewa idanunsu irin ci gaban da aka samu a asibitin.
Mun kuma ga Gadaje irin na zamani masu amfani da na’urorin zamani wanda mara lafiya ko Likitoci ko masu aikin jinya za su iya yin amfani da su domin a dago mara lafiya idan ya na kwance, nan ma ba batun maganar ba wutar lantarki domin akwai na’urorin ajiye hasken wutar lantarki a samu wutar a koda yaushe.
Kuma duk wadannan gine ginen da na’urorin kula da kiwon lafiya na zamani an samar da su ne a kasa da watanni biyu kamar yadda wani jami’in asibitin ya shaida mana.
An kuma kai mu har cikin dakin ajiyar kayayyakin asibitin wanda katafaren wurin ajiya ne mun kuma ganshi makare da kayayyaki irin na zamani duk za a Sanya su a wuraren da ake kokarin kammala ginin a halin yanzu.
Mun kuma zagaya inda Farfesa Abdulkareem Jika Yusuf ya kara gina sababbin ajujuwa domin karatun dalibai da ke neman ilimin kwarewa wajen fannin kwakwalwa, domin mun ga dalibai da muka yi magana da su suka shaida mana cewa sun zo ne daga Gwagwalada Abuja za su yi karatun sanin makaman aiki na sati biyu, an dai kammala Ajujuwan an Sanya kujerun zama da Tebura a cikin Ajujuwan.
Kuma mun ganewa idanun mu aikin gina dakunan kwanan dalibai na makarantar da ake gina wa a halin yanzu dakunan kwana guda Arba’in (40).
Mun kuma ga inda ake gina babban katafaren wurin zaman marasa lafiya irin na alfarma ga duk wanda ya samu kansa cikin halin damuwa,tabin kwakwalwa da dai irin matsalar da asibitin kan iya magancewa, ana ginin alfarma domin biyan bukatar jama’a.
Akwai kuma wani ginin da shi ma an kusa kammala shi da za a ajiye marasa lafiyar kwakwalwa wanda ba batun mara lafiya ya ce zai ta fi gina don kawai ya na samun sauki, wanann Ginin an kusa kammala shi ayi bikin budewa.
Mun kuma ga sababbin motocin daukar marasa lafiya da asibitin ya sayo manya manya irin na zamani da ke dauke da duk abin da ake bukatar a samu a wadannan motocin domin kula wa da marasa lafiya.
An kuma kammala ginin wurin kula wa da marasa lafiya na gaggawa wanda katafaren gini ne bene, ha kuma babban ofishin gudanar da mulki da babban wurin masu ilimin sanin Magunguna da duk an kammala wurin a halin yanzu sai batun fara amfani da shi kawai ya rage.
Mun kuma ga wani babban gida a cikin harabar asibitin da yakamata shi Farfesa Abdulkareem Jika Yusuf yakamata ya zauna tare da iyalansa amma ya mika wannan gidan ga dalibai mata masu zuwa karatu ko koyon sanin makamar aiki domin kare lafiya da samun natsuwar yin abin da suka zo yi.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.