Home / News / Senator Abu Ibrahim Bai Yi  Taro Da Dattawan Arewa Domin Asiwaju Bola Tinubu Ba

Senator Abu Ibrahim Bai Yi  Taro Da Dattawan Arewa Domin Asiwaju Bola Tinubu Ba

 

 

Mustapha Imrana Abdullahi

 

 

A wani rubutun da ake yadawa da bashi da tushen wanda ya rubuta shi kuma babu wanda ya Sanya masa hannu da ke tabbatar da cewa labarin karya ne ake yadawa a kafar Sada zumunta da WhatsApp, da ake yada cewa wai Sanata Abu Ibrahim ya shirya taro da Dattawan Arewa domin Asiwaju Bola Tinubu, duk da cewa har yanzu batun takararsa babu tabbacin hakan domin ba a tattauna hakan ba.

 

 

Rubutun da ake yadawa cewa wai Tinibu ya tsaya kai da fata a cikin taron wai zai dauki musulmi a matsayin mataimakin shugaban kasa da za su yi takara da shi kuma wai zai dauke shi ne daga yankin arewacin Najeriya wanda wai hakan na nuni da cewa ba a damu da kuri’un yankin Kudu maso Kudu da Kudu maso Gabas.

 

Amma dai tun asali Sanata Abu Ibrahim bai yi niyyar yi wa duniya bayani irin wannan ba, domin kada lamarin ya zama lamar ya na yin martani ne ga wani ko wasu mutane,amma bayanin hakan na da amfani kwarai matuka saboda wannan batu na yin takara ba a ma ko kai ga bayyanar da shi a fili ba ga jama’a, saboda haka Sanatan ke bayani filla- fills kamar hakan.

* Shi bai shirya wani taro da Dattawan Arewa ba domin Asiwaju Tinubu ko kuma da duk wani mutum domin hakan.

 

* Babu wani taro da Datyawan arewa da ya taba faruwa ba sabanin  yadda wasu ke yin bayanin hakan. Kuma a matsayinsa  a Dattijo a Arewa, zai Sani in ma har an yi wani taro makamancin hakan.

 

* Sanata Abu Ibrahim yakasance a matsayin aboki ga Asiwaju Tinubu taawon sana da shekaru 30 don haka ya san Asiwaju Tinubu kwarai da gaske don haka ba mutum ne da zai yi amfani da batun addini ko kabilanci ba domin ya yi takarar shugaban kasa.

 

* Asiwaju Tinubu ba zai fifita wani bangare ko gungun wasu mutane a kan wasu ba, sabanin irin yadda wannan bayanin karya da aka rubuta yake yawo a yanar Gizo da ke alamta cewa kamar ya yanke hukuncin ya fifita wasu a kan wasu, hakika lamarin babu kamshin gaskiya a cikinsa.

Asiwaju kamar yadda kowa ya Sani dan kishin kasa ne da ke da kyakkyawar mu’amalla da dukkan bangarorin kasar nan kuma ya na da abokai daga yankunan Kudu maso Kudu da Kudu maso Gabashin Najeriya da kuma sauran yankuna gida uku na Arewa maso Yamma, arewa maso Gabas da kuma Arewa ta tsakiya.

 

* Kuma ya dace a Sani cewa mun san wadanda suke da hannu game da yada wannan bayanin karya. Amma duk da haka a yanzu dai ba za mu bayyana sunayensu ba, don haka muna rokonsu da su hakura har sai lokaci ya yi tukuna kafin su fara yada bayanansu na kanzon kurege, na kage da batanci.

 

Muna bayar da shawara ga mutanen mu da kada su amince da wannan labarin karya da ake yadawa da bashi da tushe balantana makama.

 

Sa hannu

OTUNBA BIODUN AJIBOYE

Daraktan yada labarai na CNNI

A madadin Sanata Abu Ibrahim.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.