Related Articles
Mustapha Imrana Abdullahi
Rahotannin da muke samu daga Jihar Katsina na cewa mutumin da ake zargi da yana dauke da cutar Daukewar Lumfashi da ake kira Corona virus ko Covid 19.
Kwamishinan kula da harkokin lafiya na Jihar Katsina Injiniya Nuhu Yakubu Danja ne ya tabbatar wa da kafar yada labarai ta Katsina Pist haman a ofishinsa.
Da wakilinmu ya tuntubi kwamishinan lafiya na Jihar Katsina Injiniya Nuhu Yakubu Danja ya shaida ma wakilinmu cewa dama ita cutar corona virus na da wadansu Alamomi masu kamanceceniya da Alamomin wadansu cututtuka amma bayan an kammala bincike irin na Gwaje gwaje aka tabbatar cewa wanda ake zargin baya dauke da cutar, don haka ba ita bace.
Ki biyo mu domin kawo maku cikakken bayanin nan gaba kadan…