Daga Hussaini Ibrahim
Gwamnan jihar Zamfara Honarabul Bello Matawallen Maradun ya sanya hannu da tabbatar da dokar da ‘Yan majalisar Dokokin jihar suka yi na aiwatar da Kisa ga wanda aka kama da hannu cikin ‘Yan Bindiga Masu Garkuwa da mutane da masu ba ‘yan Bindiga bayanan sirri a Jihar.
Matawallen Maradun ya sanya ma dokar hannu ne ayau bayan Shugaban Majalisar dokokin jihar Muazu Magarya ya gabatar masa da Dokar a gidan gwamnatin da ke Gusau.
A cikin dokar akwai daurin rai da rai ga masu satar shanu. Kuma za’a kafa akwati na amsar koke daga jama’a a gaban gidan gwamnatin dan zamu nasara kawo karshen ‘Yan Bindiga da masu Garkuwa da mutane.
Gwamna Matawallen ya yi kira ga jama’a da su ji tsoran Allah wajan bada bayani siri a cikin wannan akwatin da Gwamnatin ta ajiye.
Shugaban Majalisar dokokin jihar Zamfara, Honarabul Muazu Magarya ya bayyana cewa, sun yi wadannan dokokin ne da nufin samarwa al’ummar jihar Zamfara mafita mai dorewa.