Home / News / Zan Iya Sadaukar Da Rayuwata Saboda Matawalle – Dokta Suleiman Shinkafi

Zan Iya Sadaukar Da Rayuwata Saboda Matawalle – Dokta Suleiman Shinkafi

Imrana Abdullahi Daga Shinkafi
Dokta Suleiman Shu’aibu Shinkafi, mai bayar da shawara ga Gwamnan Jihar Zamfara a kan harkokin hulda da kasashen waje da kuma cikin gida ya bayyana cewa zai iya sadaukar da rayuwarsa saboda kare martaba da mutuncin Gwamna Muhammadu Bello Matawalle.
Gwamna Muhammadu Bello Matawalle, mutum ne jajirtaccen mai kishin al’ummar da yake yi wa jagoranci domin idan mutum ya matsa kusa da Gwamnan Jihar Zamfara Matawalle zaka fahimci hakan, saboda haka ni na matsa kusa da shi na kuma fahimce shi kwarai.
Suleiman Shu’aibu Shinkafi ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da kungiyar da ke yada manufofin Gwamna Matawalle a kafafen Sada zumunta na zamani.
Ya ce hakika Gwamna Matawalle ya kasance wata kyautar da Allah ya ba Jihar Zamfara da ba a taba samun irin ta ba a Jihar baki daya.
” Sai da  na zo kusa da shi sannan na san hakan, domin lokacin da na zo kusa da shi sai na ga lallai shi shugaba ne mai kishin jama’asa da ya dace kowa ya sallama masa”. Inji Sarkin Shanun Shinkafi na farko.
“Ina tabbatar maku cewa hakika zan iya bayar da rayuwata wajen kare martaba da mutuncin Gwamna Matawalle, domin ya cancanci hakan a waje na saboda na samu abin da a can kafin ya nada ni a gaskiya ba ni da shi.
A game da zamana shugaban karamar hukumar Shinkafi kuwa ” wannan wani abu ne daga Allah don haka ba zan yi gardama ko sa’in sa da kowa ba a karamar hukumar Shinkafi, don haka idan ma ina son in yi rigima da wani sai in ta fi can wani wuri amma ba a nan ba, domin fata na in ga ci gaban Shinkafi ne tare da jama’arta baki daya”.
Ya kara da cewa fata na shi ne in yi maganin matsalar rashin aikin yi, kuma zan iya yin amfani da kungiyoyi masu zaman kansu wajen samun wannan nasarar domin za mu iya yin amfani da kamfanoni kamar kamfanin Nisan na yi taron tattauna wa da su har sun ce za su bani motocinsu kirar Bus , da za a rabawa masu son yin aikin harkokin sufuri da motocin da za a iya samun makudan kudade a kowane wata.
Da akwai hanyoyin da karamar hukuma za ta samu kudi, wanda idan mutum na son yin amfani da kwakwalwarsa za a iya samun abin da kowa zai amfana da shi.
” zan iya kawo kamfanin Tumatur su ba manoma duk abin da suke bukata bayan sun samar da Tumatur din sai a ba kamfanin su sarrafa ayi amfani da shi a fadin duniya cikin Najeriya da kasashen waje.
Muna da abubuwa da yawa da za mu yi amfani da su wajen taimakawa jama’a, hakika ina da kudirorin da yawa da nake son in yi wa karamar hukumar Shinkafi.
Ya dace in kara maku kwarin Gwiwar yin shirin samun horon sanin makamar aiki domin kuna kokarin dabbaka manufofi da martabar Gwamnan Jihar Zamfara ne kuma ina shaida maku cewa duk lokacin da kuke ganin ya dace ku zo domin neman taimako kofa ta a bude take kawai ku kwankwasa kofa kawai.
Na baku taimakon naira dubu Hamsin ku sayi katin da zaku yi amfani da su wajen sayen katin shiga yanar Gizo, na kuma baku turamen Atamfa domin ko kuna da mambobi mata.
” Ku tabbatar kun fadakar da jama’a su zabi jam’iyyar APC domin samun Matawalle da Sanata Sahabi Ya’u, Tsohon Gwamna mai neman kujerar dan majalisar Dattawa da dukkan wadandabza su yi takara a karkashin APC”.
Daukacin yayan kungiyar sun bayyana godiyarsu ga Dokta Suleiman Shu’aibu saboda yadda yake kokarin taimaka masu

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.