Home / News / Babu Wata Jam’iyya Sai APC A Shinkafi – Halilu Bama

Babu Wata Jam’iyya Sai APC A Shinkafi – Halilu Bama

Imrana Abdullahi Daga Shinkafi
Shigaban jam’iyyar APC reshen karamar hukumar shinkafi Alhaji Ibrahim Halilu Bama, ya bayyana cewa a iya saninsu babu wata jam’iyya a karamar hukumar Shinkafi sai APC kawai.
Halilu Bama ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gabatar da jawabinsa a wajen wani kwarya kwaryar taron rabon kayan Romon Dimokuradiyya ga al’ummar Shinkafi Mazauna Legas da aka yi a garin Shinkafi.
Alhaji Halilu Bama, ya ci gaba da cewa kasancewar jam’iyyar APC a matsayin gagarumar jam’iyyar ceton Talakawa da ke aiki tukuru wajen inganta rayuwar al’ummar birni da karkara, saboda haka ya dace kowa ya ci gaba da bayar da cikakken hadin kai da goyon baya domin samun sukunin ciyar da al’umma gaba har a kai ga Tudun muntsira.
Motar da aka ba yan Shinkafi Mazauna Legas
“Muna tabbatar maku cewa babu wata jam’iyya a halin yanzu da ta wuce APC”.
Ya lissafa dimbin abubuwan alkairin da Dokta Suleiman Shu’aibu Shinkafi yake yi wa jama’a a karamar hukumar Shinkafi da suka hada da taimakawa domin yin aikin hanya, Gina Masallatai, taimakawa jama’a Maza da mata da Injunan Nika da na Taliya, Turamen Atamfofi ga kuma kyautar mota kirar Honda ga al’ummar Shinkafi Mazauna Legas da sauran abubuwa”.
Sai kuma yin kira ga daukacin matasa da du tabbatar da bayar da cikakken hadin kai da goyon baya ga jam’iyyar APC da dukkan yan takararta baki daya domin su samu nasara”.
Hakazalika ya bayyana irin abubuwan alkairin da Sanata Sahabi Ya’u Kaura, ke aiwatarwa ga jama’ar Mazabarsa da suka hada da Gina Tijiyoyin Zamani domin yin Noma, Fitulun kan hanya da ke amfani da hasken rana da dai sauran muhimman ayyukan ci gaban rayuwar jama’a.
.
Sani Galadima Garkuwan Shinkafi, ya tabbatarwa da jama’a a wajen taron cewa Gwamnan Jihar Zamfara Muhammadu Bello Matawalle na bayar da kudi kuma a irin yadda yake bayar da kudin tsawon watanni Shida da suka gabata haka yake bayarwa ga kananan hukumomi don haka duk wata ke yin magana sabanin hakan ba gaskiya bane.
” Akwai ranar yi wa duniya jawabi idan an hau Duro, saboda kyakkyawan ayyukan da ake gudanarwa ya sa a hali yanzu babu wata jam’iyya sai APC don haka a bata cikakken hadin kai da goyon baya a koda yaushe.
Da yake gabatar da jawabi Shugaban jama’ar Shinkafi mazauna Legas Alhaji Nasiru Muhammad cewa ya yi hakika sun kammala shirin bayar da cikakken hadin kai da goyon bayansu ga jam’iyyar APC da dukkan wadanda suka tsaya mata takara da nufin samun nasarar da ake bukara.
Da yake gabatar da jawabi mai gayya mai aiki dan takarar neman jam’iyyar APC  ta tsayar da shi takarar shugaban karamar hukumar Shinkafi, Dokta Suleiman Shu’aibu Shinkafi, kira ya yi ga jama’a da su ci gaba da bayar cikakken hadin kai da goyon baya ga APC domin samun biyan bukatar kowa.
“Idan kun zabe ni a matsayin shugaban karamar hukumar Shinkafi zan tabbatar da kare mutunci da martabar jama’a kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanadar, kuma Za’a samu ayyukan raya kasa da yawa a birni da karkarar karamar hukumar Shinkafi”.
Za mu yi aiki a bangaren ilimi, lafiya, kula da jin dadi da walwalar jama’a, bunkasa harkar Noma da Kiwo da kuma samar da tsaron lafiya da dukiyar jama’a.
“Na bayar da wannan motar ne ga yan uwa al’ummar Shinkafi mazauna Legas domin kara karfafa masu Gwiwa su ci gaba da nuna Soyayya da biyayya ga jagoran mu tsohon Gwamna Mahmuda Aliyu Shinkafi da jam’iyyar APC karkashin jagorancin Gwamna Dokta Bello Muhammad Matawalle.
Kuma muna fatan zaku ci gaba da fadakar da jama’a irin alkairin da ke tattare da gagarumar jam’iyyar APC a Najeriya baki daya
Tun da farko dai an nuna wa yayan jam’iyyar APC muhimmancin da ke akwai na zaben jam’iyyar APC tun daga sama har kasa wato daga kan Bola Ahmad Tunubu har zuwa kasa a matakin mazaba duk a zabi APC lungu da sako.

About andiya

Check Also

KADCCIMA ON  ON REVIEW OF ELECTRICITY TARIFF

    Following approval by the Electricity Regulatory Commission (NERC) for the increase of electricity …

Leave a Reply

Your email address will not be published.