Home / KUNGIYOYI / KU ZABI GWAMNA MUHAMMAD BELLO MATAWALLE – SULEIMAN SHU’AIBU SHINKAFI

KU ZABI GWAMNA MUHAMMAD BELLO MATAWALLE – SULEIMAN SHU’AIBU SHINKAFI

…Suleiman Shinkafi Ya halarci taron Yan asalin Jihar Zamfara a Kaduna
…Domin Ci Gabab Al’umma
IMRANA ABDULLAHI DAGA KADUNA
 Dokta Suleiman Shu’aibu Shinkafi, ya bayyana kungiyar al’ummar Zamfarawa mazaunan Kaduna da cewa wani babban abin alkairi ne saboda haka a madadin mai girma Gwamnan Jihar Zamfara Muhammadu Bello Matawalle, bayyana farin cikinsa ya yi da halartar wannan taron na al’ummar Jihar Zamfara mazauna Kaduna.
Gwamnan Jihar Zamfara ya ba ni Umarnin cewa in ta fi wasu Jihohi domin ganawa da yan asalin Jihar Zamfara da ke zaune a can su na neman abincinsu, domin in fadakar da su muhimmancin dawowa Gida a yi zabe, muhimmancin bin dokokin wuraren da suke zaune da kuma ci gaba da yin rikon abin yi domin dogaro da kai.
“Ni zan yi amfani da wannan damar da nake da ita in zama gatan al’ummar Jihar Zamfara a ko’ina suke a cikin kasar nan, kowa ya  san ni ba ni tare da Gwamnati amma saboda na amince da wannan Gwamnati da akidunsu ya sa na shiga cikin wannan Gwamnatin.
Gwamna Matawalle mutum ne jajirtacce ne musamman wajen taimakawa jama’a, domin ya na son ci gaban kowa.
“Gwamnatin Dokta Bello Muhamamd Matawalle na tare da wannan kungiyar don haka idan ina cikin wannan Gwannatin kuma Gwamna na matsayin Gwamna ma za a mance da ku ba, domin wannan Gwamnatin na tare da ku”.
Ina shaida maku cewa ku dauki kan ku a matsayin jakadun Gwamnatin Jihar Zamfara a duk inda kuke, ku zabi Gwamna Muhammad Bello Matawalle, domin ya ci gaba da aiwatar da ayyukan alkairi ga jama’a.
Dokta Suleiman Shu’aibu Shinkafi, ya bayyana shugaban wannan kungiya a matsayin jajirtaccen mutum da ke da kishi Jama’a
“Na amince na karbi babban Uban wannan kungiyar, son haka ina cikin wannan kungiyar”.
Wannan kungiyar ta yi gata domin kowa na zaune a cikin garin Kaduna.
“Duk wanda yake da aniyar yin takara a wata jam’iyya ya fito ya gaya mana domin a taimaka masa a kai ga ga ci, karkashin jagorancin Gwamna Muhammadu Bello Matawalle”.
Akalla za a dauki mutane biyu da za a ba mukamin SSA da za su aiki a matsayin jakadun jama’ar Jihar Zamfara don haka zabi ya rage gare ku, ku zabi wanda zai yi wannan aikin.
Malam Ibrahim Musa Jan bako, a jawabinsa a wajen taron cewa ya yi a matsayinsu na yayan Jihar Zamfara sun yi Imani da kudirin cewa “Za mu ba Gwamnati cikakkrn hadin kai da goyon baya ga Gwamna Matawalle da Gwamnatinsa.
Muna da dimbin ma’adinai a yankunan mu da ya fi na kowa don haka Gwamnati ta tashi tsaye wajen taimakawa jama’ar kasa.
Talatar Mafara, Maru da Bakura akwai dimbin arziki sosai
“A Kaduna muna da majalisu nan cikin garin Kaduna a Unguwanni irin Unguwar Mu’azu, Bakin Ruwa da su Unguwar Sanusi da sauran wurare da yawa”.
“Tun da dai a yanzu Gwamnati ta san muhimmancin mu hakika muna godiya kwarai da wannan
Ya ku masu imani kuji tsoron Allah domin sai kowa Allah ya tayar da shi a gaba gare shi a ranar Lahira.
Malam Ibrahim Kauran Namoda, Sarkin Shanu hakika mutum ne mai kokari da son al’umma baki daya.
“Duk yawan jama’ar nan babu cima zaune kowa ya na da sana’arsa ta neman abin kai, don haka su na kokarin neman tallafin jari ta yadda sana’arsu za ta kara bunkasa kuma sun cancanci wannan tallafi”.
A ma’aikatar bayar da tallafin Najeriya, Sa’adiyya Umar Faruk, yar Jihar Zamfara ce don haka a taimaka wa wadannan mutanen yayan Jihar Zamfara
A cikin yayan wannan kungiya akwai wadanda suka kammala karatunsu kuma su na dauke da satifiket na karatu daban daban su na neman tallafin aiki da dai sauran al’amura daban daban.
“Kunguyar ta ba Dokta Suleiman Shu’aibu Shinkafi, babban Uban wannan kungiya
Daga cikin wadanda suka gabatar da jawabi akwai Honarabul  Muhammad Namanga da Malam Yahaya Katuru da kuma Malam Basiru Shu’aibu Shinkafi duk sun bayyana cikakken farin cikinsu da irin ayyuka da kokarin wannan kungiyar.
Sarkin Shanun Shinkafi na farko hakika mutum ne jajirtaccen da ke kwato hakkin dan Adam.
Ko lokacin da Dokta Suleiman ya na zaune a garin Abuja ya san waje Sarkin Shanu da irin ayyukan da yake yi na taimakon jama’a.
Daukacin yayan asalin Jihar Zamfara sun tabbatar da cewa sun fara tafiyar ganin Gwanna Muhamamdu Bello Matawalle ya samu nasara tun daga yanzu har illa masha Allahu.
Hon Nasiru usman Kaura Takurus, ya bayyana Sarkin shanu a matsayin wanda zai taimaka wa kungiyar.
Hassan Sa’adu shigaba da ya yi jawabin godiya a bayan taron inda ya tabbatar wa da Gwamnati cewa za su bayar da cikakken hadin kai da goyon baya ga Gwannatin Muhammad Bello Matawalle domin a samu nasarar da kowa ke bukatar samu
Salisu Ibrahim mataimakin shugaba shima yaba wa Gwamnatin Dokta Muhammad Bello Matawalle ya yi bisa Namijin kokarin da take yi wajen inganta rayuwar jama’a.

About andiya

Check Also

Oil Producing Communities Group threatens to seal all Oil pipeline facilities over poor treatment of Dangote, other Modular Refineries

…Warn IOCs against economic sabotage …Urge FG to end fuel, diesel importation The Host Communities …

Leave a Reply

Your email address will not be published.