Home / Labarai / Al’amura Sun Dai- daita Kan Hanyar Kaduna Zuwa Abuja 

Al’amura Sun Dai- daita Kan Hanyar Kaduna Zuwa Abuja 

Imrana Abdullahi Daga Kaduna
Biyo Bayan irin tsaiko da jerin Gwanon motocin da aka samu a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja a halin yanzu duk al’amura sun dai- daita domin hanya ta bude ana wucewa ba tare da wata matsala ba.
Bayan kwashe wadansu kwanaki ana aiki tsakanin Gwamnatin Jihar Kaduna, Kamfanin Julius Beger, Rundunar sojoji da sauran hukumomi an samu nasarar warware matsalar cinkoson ababen hawa da aka samu a dai – dai Kateri kan titin Kaduna zuwa Abuja, wanda a halin yanzu ababen hawa na tafiya lafiya kalau.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwar da ke dauke da sa hannun Malam Samuel Aruwan kwamishinan kula da harkokin tsaro da al’amuran cikin gida na Jihar Kaduna.
Takardar ta ci gaba da bayanin cewa a halin yanzu hanya ta bude sosai babu wani cinkoson ababen hawa a tsakanin kilomita 75 kan babban titin Kaduna zuwa Abuja, bayan da aka samu lalacewar wata babbar motar daukar kaya ta Turela a kan hanyar.
Gwamnatin Jihar kaduna na bayar da hakuri ga daukacin al’umma na matsalar da aka samu sakamakon wannan tsaikon wanda ya haifarwa da jama’a shiga cikin wani mawuyacin hali na wasu yan kwanaki.
Zakalika Gwamnatin Jihar Kaduna na godiya ga jami’an tsaro da suka yi tukuru ba dare ba rana na ganin al’umma sun samu tsaron lafiya tare da dukiyarsu baki daya.

About andiya

Check Also

KASUPDA EMBARKS ON SENSITIZATION EXERCISE TO PEOPLE ON INFORMAL ACTIVITIES

  Kaduna State Urban Planning and Development Authority(KASUPDA) has commenced on the sensitization programme to …

Leave a Reply

Your email address will not be published.