Home / Labarai / A Biya Yan Jarida Miliyan Dari Da Hamsin

A Biya Yan Jarida Miliyan Dari Da Hamsin

Imrana Abdullahi
Wani dan kasuwa kuma Malamin addinin musulunci ya bayyana cewa yana da matukar muhimmanci ga wanda ya zazzagi dan jaridar da ke aiki da kamfanin daily trust a biyasu naira miliyan dari da Hamsin (150,000,000) domin kada wani ya sake cin mutuncin dan jarida da ke aiki domin jama’a.

Shehu Ayatullah Dallatun Unguwar Shanu, ne ya yi wannan kiran lokacin da yake ganawa da manema labarai a cibiyar yan jarida ta kasa reshen Jihar kaduna.
Dallatun unguwar Shanu ya bayyana manema labarai a matsayin masu yin aiki domin jama’a don haka babu wani mutum da zai mike tsaye haka kawai ya ci mutuncin yan jarida haka kawai.
“Musamman idan aka yi la’akari da cewa su yan jarida ba mutane bane da ke rike da makami, kuma suna zuwa wuraren yaki,manya manyar taro na duniya da wuraren da ake samun wata takaddama a tsakanin jama’a ko’ina a fadin duniya”.
Ya ci gaba da bayanin cewa ya dace a samar da wata hanyar biyan diyya ha yan jarida, saboda su daga su sai kayansu na aiki, amma ba makami ba.
Ya kuma kara fadakar da yan jarida cewa su dauki matakin kin yi wa duk wanda ke son takawa yan jarida da kada su yi masa aiki wanda in sun yi hakan za su samu daraja da martabar da ya dace su ssmu a tsakanin al’umma.

About andiya

Check Also

Dangote crashes Diesel price to N1,000 per litre

In an unprecedented move, Dangote Petroleum Refinery has announced a further reduction of the price of diesel from …

Leave a Reply

Your email address will not be published.