Home / Labarai / Gadar Rugachikun Kusa Da Kasuwar Duniya Ta Kaduna Ta Lalace

Gadar Rugachikun Kusa Da Kasuwar Duniya Ta Kaduna Ta Lalace

 Imrana Abdullahi
Kamar yadda zaku iya gani a cikin hotunan da ke cikin wannan labarin Gadar da ke dai dai Kasuwar duniya ta kasa da kasa da ke Kaduna ta lalace sakamakon ruwan sama mai nauyi da ake yi a wannan Daminar.
Ita dai wannan Gadar tana da matukar amfani a duk fadin tarayyar Nijeriya baki daya saboda ita ce hanyar da ke hada yankin arewacin Njeriya da sauran sassan kasar, har ma da wadansu sassa na wadansu kasashen da ke Makwabtaka da Nijeriya.
Kamar dai yadda zaku iya gani a cikin hotunan nan a halin yanzu motoci manya da kananan duk sun koma bin hannu daya a madadin yadda hanyar take a can baya mai zuwa ba ruwansa da masu Dawowa.
A halin yanzu dai jama’a da dama na nuna fargabarsu a game da lalacewar Gadar, saboda irin matsanancin jerin Gwanon motocin da za a iya samu a wannan hanya.
Saboda a bara ne aka rika samun matsanancin jerin Gwanon motoci manya da kanana sakamakon aikin hanyar da ake yi daga Abuja zuwa Kano, wanda idan matafiya sina zo inda ake gyaran hanyar shikenan sai abin da Allah yaso.
Saboda matafiya sun rika makalewa a cikin jerin Gwanon motoci wanda sanadiyyar hakan har kwana suke yi a kan layi.
Kuma wani al’amarin ma shi ne na rashin tsaro ga kuma irin hadarin da aka rika samu saboda gyaran hanyar wanda sanadiyyar hakan har aka rika rasa rayukan jama’a da dama.

About andiya

Check Also

NASCON grows turnover by 37%, assures Shareholders of Continuous Growth, Value Creation

NASCON Allied Industries Plc has assured its shareholders of continuous growth and value creation in …

Leave a Reply

Your email address will not be published.