Home / Labarai / A Gaggauce An Kama Kasurgumin Mai Sata Da Kashe Mutane

A Gaggauce An Kama Kasurgumin Mai Sata Da Kashe Mutane

Mustapha Imrana Abdullahi

A kokarin jami’an tsaron tarayyar Najeriya na ganin sun magance dukkan matsalar tsaron da ake fama da ita na satar jama’a domin karbar kudin fansa da kuma satar Dabbobi wanda duk hakan ke yin sanadiyyar salwantar Dukiya da rayukan jama’a, a halin yanzu rahotannin da muke samu na tabbatar mana da cewa an yi nasarar kame wani Kasurgumin mai satar jama’a da ake kira da Turji da ya addabi jihohi da yawa.

“Yanzun Nan An Cafke Kasurgumin Dan Bindigar da Ya Addabi Jihohin Sokoto, Zamfara Katsina da Kuma Niger”

Rahotanni dake zuwa mana yanzu na nuna cewar, jami’an tsaro sun sami nasarar cafke shahararren dan fashin nan kuma dan bindiga Bello wanda ake masa lakabi da (Turji Gudde) a jihar Zamfara.

Rahotannin sun bayyana cewar, kasurgumin dan bindigar ya hallaka sama da mutane dubu daya tsakanin jihohin Sokoto, Katsina, Zamfara, da yankin jihar Niger wanda bai dauki rayuwar mutane komai ba.

About andiya

Check Also

KASUPDA EMBARKS ON SENSITIZATION EXERCISE TO PEOPLE ON INFORMAL ACTIVITIES

  Kaduna State Urban Planning and Development Authority(KASUPDA) has commenced on the sensitization programme to …

Leave a Reply

Your email address will not be published.