Home / Labarai / Yan bindiga Sun Sace Matar Dan Majalisa Da Yayansa Biyu

Yan bindiga Sun Sace Matar Dan Majalisa Da Yayansa Biyu

Mustapha Imrana Abdullahi
Wadansu mutane da ake zargin cewa yan bindiga ne masu satar mutane sun kai hari garin Kurami da ke karamar hukumar Bakori a Jihar Katsina da misalin karfe 8: 30 na daren ranar jiya Asabar.
Bayanan da muke samu na cewa yan bindigar sun sace uwargidan dan majalisar da yayansa biyu.
Dokta Ibrahim Kurami shi ne dan majalisa mai wakiltar al’ummar karamar hukumar Bakori a majalisar dokoki ta Jihar Katsina
Wata majiya daga garin Kurami ta shaida wa wakilin mu cewa yan bindigar sun harbi wani mutum mai aikin bayar da agajin gaggawa mai suna Ubaida Usman da inda yake can ana duba lafiyarsa a yanzu haka.
Majiyar mu ta bayyana sunan uwargidan dan majalisar da aka sace kamar haka Rabi’atu Ibrahim, da yayan biyu masu suna ABBA da Khalifa Ibrahim.

Kamar dai yadda majiyar ta bayyana cewa yan bindigar sun Isa garin Kurami ne inda suka rika yin harbin kan mai uwa da wabi da misalin karfe 8: 30 na dare.

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoton babu wani bayani ko sanarwa daga hukumomin Gwamnati a matakin karamar hukuma, Jiha ko a bangaren jami’an tsaro da suka fitar.

Wannan lamari dai na satar iyalan dan majalisar ya faru ne akalla shekara daya da sace shi kansa mai gidan inda aka sake shi bayan biyan kudin fansa.

About andiya

Check Also

Majalisa Ce Ta Bambanta Dimokuradiyya Da Mulkin Karfa Karfa – Ado Doguwa

  …Sai An Ba Kananan hukumomi Yancinsu   Bashir Bello majalisar Abuja Honarabul Alhassan Ado …

Leave a Reply

Your email address will not be published.